Dan sandan da 'yan bindigan daji suka harba ya sheka lahira a asibiti

Dan sandan da 'yan bindigan daji suka harba ya sheka lahira a asibiti

- Dan sandan da 'yan bindiga suka harba a garin Tsamiya jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya

- Hardo mai mukamin DSP na jagorantar rundunar ne yayin da suka yi musayan wuta

- Harbin da 'yan bindigan suka mishi ya shiga kashin kafarsa kuma ya karya shi

Dan sanda mai mukamin DSP mai suna Abdulqadir Garba Hardo, wanda wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka harba a jihar Kebbi ya riga mu gidan gaskiya.

Hardo wanda 'yan bindiga suka harba a kafa yayin da yake jagorantar rundunar sun yi musayar wuta da 'yan bindigan a garin Tsamiya dake karamar hukumar Bagudo ta jihar.

Raunin da ya samu daga harsashin ya ratsa ta kashin kafarsa inda ya karya shi kuma ya rasu a wani asibiti dake Gusau, jihar Zamfara a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, wanda ya tura wakilai domin jana'izar mamaci, ya bada kyautar N2 miliyan ga iyalan dan sandan.

KU KARANTA: Nasrun Minallah: Dakaru sun sheke 'yan bindiga 53, kwamandojinsu 5 a jihar Zamfara

Dan sandan da 'yan bindigan daji suka harba ya sheka lahira a asibiti
Dan sandan da 'yan bindigan daji suka harba ya sheka lahira a asibiti. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kano: Barkewar amai da gudawa ta janyo rasa rayuka 15, 40 suna asibiti kwance

A wata takarda da mai bada shawara na musamman ga Gwamnan a fannin yada labarai, Yahaya Sarki ya fitar, ya ce Bagudu ya kwatanta Hardo da zakakurin dan sanda mai aiki cike da kwarewa.

Gwamnan yayi addu'ar Allah ya jikansa da rahama kuma Allah ya baiwa iyalansa hakurin jure rashinsa.

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Babale Umar, wanda yayi jawabi a madadin Gwamnan, ya sanar da cewa Gwamnan jihar Kebbi ya sha alwashin cigaba da tallafawa iyalansa.

An yi jana'izar marigayin a gidansa kuma an birne shi a makabartar Unguwar Gwaza dake Gusau. An haifa marigayi AbdulQadir Garba Hardo a ranar 13 ga watan Oktoban 1979 kuma ya shiga aikin 'yan sanda a 2012.

A wani labari na daban, 'yan bindiga da ake zargin mambobin IPOB ne sun kai mugun farmaki ofishin 'yan sanda dake Odoro Ikpe a karamar hukumar Ini ta jihar Akwa Ibom.

Jami'ai shida sun rasa rayukansu a harin da aka kai a sa'o'in farko na ranar Asabar, 8 ga watan Mayu, The Punch ta ruwaito haka.

Hakazalika, a yayin bada rahoton harin, The Cable ta ce wannan ne karo na biyu da ake kai hari cikin mako daya a jihar ta kudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel