Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada ranakun Laraba da Alhamis hutun Sallah

Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada ranakun Laraba da Alhamis hutun Sallah

- Gwamnatin tarayya ta bada ranakun Laraba da Alhamis daidai da 12 da 13 ga watan Mayun 2021 a matsayin hutun sallah

- Ministan al'amuran cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar a garin Abuja

- Yayi kira ga 'yan Najeriya dake gida da ketare da su yi amfani da wannan damar wurin addu'ar zaman lafiya a fadin kasar nan

Gwamnatin tarayya ta bayyana Laraba, 12 da Alhamis 13 ga watan Mayun 2021 a matsayin hutun sallah karama mai zuwa.

Ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, ya bada wannan sanarwar a madadin gwamnatin tarayya a Abuja a ranar Litinin, The Nation ta ruwaito.

Ya taya Musulmi murnar zuwan sallah tare da kira ga 'yan Najeriya dake gida da ketare da su yi amfani da wannan lokacin wurin yin addu'ar zaman lafiya, daidaituwa da kuma habakar tattalin arzikin kasar nan.

A wata takarda da Aregbesola ya fitar kuma sakataren ma'aikatarsa, Dr Shuaib Belgore yasa hannu, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su kasance masu bin doka tare da kaunar juna, juriya, hakuri da ladabi kamar yadda Annabi Muhammad ya koyar.

KU KARANTA: Nasrun Minallah: Dakaru sun sheke 'yan bindiga 53, kwamandojinsu 5 a jihar Zamfara

Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada hutun Laraba da Alhamis
Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta bada hutun Laraba da Alhamis. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Hankula sun tashi a Onitsha bayan babbar mota dauke da harsasai ta fadi a titi

Ya yi kira ga hukumomin tsaron kasar nan da su kasance masu jajircewa da kishin kasa a yayin da suke yaki da barkewar rashin tsaro da sauran al'amuran ta'addanci dake faruwa a kasar nan.

Ya tabbatar da cewa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari za ta kawo karshen wannan barkewar ta'addancin kuma za ta dawo da zaman lafiya a kowanne sako da lungun kasar nan.

A wani labari na daban, masarautar Kano ta ce za ta yi hawan gargajiya na sallah da ta sa saba yi domin shagalin bikin murnar karamar sallah a jihar.

Wannan ne zai zama hawan daba na farko da za a yi a jihar tun bayan hawan Alhaji Aminu Ado Bayero karagar mulkin Kano.

Idan za mu tuna, a 2020, gwamnatin jihar ta dakatar da yin hawan sallah saboda annobar korona da ta zagaye duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel