Da Duminsa: Ministan Abuja Ya Hana Zuwa Filin Idi a Bikin Karamar Sallah

Da Duminsa: Ministan Abuja Ya Hana Zuwa Filin Idi a Bikin Karamar Sallah

- Ministan Birnin Tarayya, Muhammad Musa Bello ya sanar da haramta gudanar da Sallar Idi a Babban Filin Idi na Kasa da ke birnin

- Sanarwar tasa na zuwa ne a yayin da al’ummar Musulmi ke shirye-shiryen Sallah Karama

- Haakan na daga cikin kokarin da ake yi na hana sake barkewar annobar korona

Daga cikin kokarin shawo kan barkewar cutar COVID-19, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Malam Muhammad Bello, ya hana yin sallar idi a babban filin Idi na kasa da ke kan babbar hanyar Umaru Musa Yar’Adua.

A cewar wata sanarwa daga Babban Sakataren yada labarai na Ministan, Mista Anthony Ogunleye, Hukumar Gudanarwar Birnin Tarayya (FCTA), ta dauki matakin ne bayan zaman da Ministan ya jagoranta da Majalisar Limaman Abuja.

KU KARANTA KUMA: Yanzu-Yanzu: Buhari Na Ganawa da Shugabannin Tsaro Bayan Yunkurin Fashi da Makami a Aso Rock

Da Duminsa: Ministan Abuja Ya Hana Zuwa Filin Idi a Bikin Karamar Sallah
Da Duminsa: Ministan Abuja Ya Hana Zuwa Filin Idi a Bikin Karamar Sallah Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Ogunleye ya ce tawagar a karkashin jagorancin Shugabanta, Imam (Dr) Tajudeen M.B Adigun, sun sadu da Bello ne domin tattaunawa kan hanyoyin da za a bi domin bikin Eid el-Fitr mai zuwa, Daily Trust ta ruwaito.

“Ana umartar mutane su yi Sallar Idi a harabar masallatan Juma’ar unguwanninsu, a kuma rage yawan masu shiga masallaci zuwa kasa da kashi 50%.

“Wajibi ne kuma mahukunta na addini su kula da shige da ficen masu ibada, su kuma tabbatar da kiyaye matakan kariya na sanya takunkumi, ba da tazara, da kuma wanke hannu.

“Bukukuwan Sallah kuma a takaita su zuwa cikin gidaje, yayin da wuraren shakatawa za su kasance a rufe,” in ji sanarwar.

Ministan ya godewa shugabannin addinin kan hadin kan da suka bayar wajen yakar COVID-19, yana mai jaddada cewa bayan an shiga cikin annoba ta farko da kuma ta biyu da ta haifar da asarar rayuka, ya zama wajibi a hana afkuwar yanayi na uku kamar yadda ake gani a wasu kasashe a fadin duniya.

Da yake magana a madadin kungiyar, Adigun ya ce “A musulinci, ana sauraren masana, wadanda kwararru ne da wadanda suka tattauna da mu a zahiri masana ne a fannin ilimin likitanci. A Musulunci, ana bin umarnin shugabanni.

KU KARANTA KUMA: Laylah Ta Karbi Rikon Wani Dan Shekara 12 da Ta Gani Yana Gararanba a Titi, Ta Sanya Shi a Makaranta

"A kan wannan da abin da muke da yakini a kai, muna kira ga al'ummar Musulmi da su girmama wannan matsaya ta Gwamnatin FCT ta hanyar yin Sallar Idi a kananan hukumominmu."

A baya mun ji cewa Gwamnatin tarayyar Nigeria ta sake dawo da dokar takaita fita a dukkan kasar daga 12 na dare zuwa 4 na asuba domin dakile yaduwar annobar korona wato COVID-19, The Nation ta ruwaito.

Mukhtar Mohammed, manaja kula da yaduwar cuta na kasa ne ya sanar da hakan yayin jawabin da kwamitin shugaban kasa kan korona ta yi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng