Wani Ango Ya Wallafa Hotunan Kasaitaccen Bikin Aurensa, an Gano Amarya Sanye da Nikabi

Wani Ango Ya Wallafa Hotunan Kasaitaccen Bikin Aurensa, an Gano Amarya Sanye da Nikabi

- Kyawawan hotunan wasu ma'aurata da suka yi aure kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar sun sha jinjina a shafin Twitter

- Yayin da wasu ba su fahimci dalilin da ya sa aka rufe fuskar matar ba, wasu kuma sun albarkaci ma'auratan da addu'o'i masu sanyaya zuciya

- Mijin ya ce yin aure yana daya daga cikin kyawawan abubuwan da suka faru a rayuwarsa

Wani matashin mai amfani da shafin Twitter, @kampo_k, ya haddasa cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan ya wallafa hotuna don jinjina wa sabuwar masoyiyarsa.

A wani sako da ya wallafa a ranar Litinin, 10 ga watan Mayu, sabon angon ya ce ya yi auren ne da burin ransa a ranar karshe ta watan Afrilun shekarar 2020.

KU KARANTA KUMA: Laylah Ta Karbi Rikon Wani Dan Shekara 12 da Ta Gani Yana Gararanba a Titi, Ta Sanya Shi a Makaranta

Wani Ango Ya Wallafa Hotunan Kasaitaccen Bikin Aurensa, an Gano Amarya Sanye da Nikabi
Wani Ango Ya Wallafa Hotunan Kasaitaccen Bikin Aurensa, an Gano Amarya Sanye da Nikabi Hoto: @kampo_k
Asali: Twitter

Hotunan bikinsa masu ban sha'awa sun sa masu amfani da shafin Twitter da dama sun taya shi murna. Sai dai kuma, waɗanda suka yi tambayoyi, suna son sanin dalilin da ya sa ma'auratan suka zabi yin irin shigar da suka yi.

Mutumin ya rubuta a shafinsa na Tweeter cewa:

"A wannan ranar a watan da ya gabata wani kyakkyawan abu ya same ni. Alhamdulilah. Na kama masoyiyata a wannan rana."

KU KARANTA KUMA: Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa Ya Nuna Sabbin Motoci 2 Masu Tsada Wanda Kudinsu Ya Kai Naira Miliyan 300

Kamar yadda yake a lokacin rubuta wannan rahoton, rubutun nasa ya tara ‘likes’ sama da 2,000 tare da martani da yawa.

Ga wasu daga cikin martanin a kasa:

@John69111879 ya ce:

"Tana da kyau. Ina taya ku murna."

@SandraAdaeze4 ta tambaya:

"Kada ku yi fushi,kawai ina so in sani don Allah. Don haka tambayata ita ce me yasa aka rufe fuskarta? Rigar ta yi kyau sosai."

@horlardoyeen ya ce:

"Rigarta tayi kyau sosai."

@AdemolaSolalu ya amsa:

"Wannan shine ainihin abin da wannan hoton yake nufin cimmawa. Ko da baka bayyana jikinka ba, kana iya zama kyakkyawa."

A gefe guda, kamar yadda aka yarda da auren mace fiye da daya a wasu kasashen, wata sabuwar dokar aure a Afirka ta Kudu na iya bawa mace damar auren fiye da miji daya kwanan nan.

Dokar na daya daga cikin wadda aka fi nuna bukata a wata takardar jin ra'ayoyin mutane akan dokar aure.

An fitar da kundin dokoki mai shafuka 67 wanda sashen kula da al'amuran zamantakewa ya fitar a satin nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel