Yanzu-Yanzu: Buhari Na Ganawa da Shugabannin Tsaro Bayan Yunkurin Fashi da Makami a Aso Rock

Yanzu-Yanzu: Buhari Na Ganawa da Shugabannin Tsaro Bayan Yunkurin Fashi da Makami a Aso Rock

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar tsaro ta kasa a fadar shugaban kasa

- Sai dai kuma zuwa yanzu babu wani cikakken bayani kan ajandar amma baya rasa nasaba da yanayin tsaron kasar

- Hakan na zuwa ne sama da awanni 24 bayan wasu barayi sun yi yunkurin kai hari gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari

A yanzu haka, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana cikin ganawa da shugabannin tsaro na Najeriya a Fadar Shugaban kasa, Abuja.

Ganawar na zuwa ne sama da awanni 24 bayan wasu ‘yan fashi da makami sun yi yunkurin kai hari gidan shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Ibrahim Gambari.

Fadar Shugaban kasar ta sanar da batun ganawar ne ta shafinta na Twitter amma ba ta bayar da cikakken bayani kan ajandar ta ba.

Yanzu-Yanzu: Buhari Na Ganawa da Shugabannin Tsaro Bayan Yunkurin Fashi da Makami a Aso Rock
Yanzu-Yanzu: Buhari Na Ganawa da Shugabannin Tsaro Bayan Yunkurin Fashi da Makami a Aso Rock Hoto: @NGRPresident
Asali: Twitter

KU KARANTA KUMA: Wani Ango Ya Wallafa Hotunan Kasaitaccen Bikin Aurensa, an Gano Amarya Sanye da Nikabi

Sai dai ana sa ran taron zai duba yanayin tsaro da kasar ke ciki a yanzu.

Taron wanda aka fara shi da karfe 10 na safe, ana yin sa ne a dakin taro na Ofishin Uwargidan Shugaban Kasa.

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Mustapha; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da kuma mai bada shawara kan harkokin tsaro, Manjo-Janar Babagana Monguno.

KU KARANTA KUMA: Laylah Ta Karbi Rikon Wani Dan Shekara 12 da Ta Gani Yana Gararanba a Titi, Ta Sanya Shi a Makaranta

Sauran wadanda suka halarci taron sun hada da Babban Lauyan kasa kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami; Ministan Harkokin Waje, Geoffrey Onyema; Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Salihi Magashi (Mai ritaya) da Ministan Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola.

A baya mun kawo cewa wasu barayi sun yi yunkurin fadawa cikin gidan shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, dake Aso Rock, birnin tarayya Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Litinin.

Garba ya bayyana cewa barayin basu samu nasarar satan komai ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel