Laylah Ta Karbi Rikon Wani Dan Shekara 12 da Ta Gani Yana Gararanba a Titi, Ta Sanya Shi a Makaranta

Laylah Ta Karbi Rikon Wani Dan Shekara 12 da Ta Gani Yana Gararanba a Titi, Ta Sanya Shi a Makaranta

- Wata 'yar Najeriya ta samu karbuwa a wajen masu amfani da shafukan sada zumunta kan halaccin da tayi wa wani yaro da ta gani a titi

- Matar ta gamu da wani yaro dan shekaru 12 a kan titi, ta dauke shi kuma ta sanya shi a makaranta

- Ta ce yaron ya sace zuciyar ta ne a lokacin da suka fara haduwa

Wata 'yar Najeriya ta karade yanar gizo sakamakon kwazonta da kuma kirkinta. Matar da aka ambata da suna Laylah Ali Othman ta sauya rayuwar wani matashin yaro yayin da ta dawo da rikonshi a hannunta.

Laylah, kamar yadda ta wallafa a shafin ta na Facebook, ta samu yaron mai shekaru 12 ne a kan wani titi a cikin birnin Abuja kuma ta tausaya masa.

KU KARANTA KUMA: Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa Ya Nuna Sabbin Motoci 2 Masu Tsada Wanda Kudinsu Ya Kai Naira Miliyan 300

Laylah Ta Karbi Rikon Wani Dan Shekara 12 da Ta Gani Yana Gararanba a Titi, Ta Sanya Shi a Makaranta
Laylah Ta Karbi Rikon Wani Dan Shekara 12 da Ta Gani Yana Gararanba a Titi, Ta Sanya Shi a Makaranta Hoto: Laylah Ali Othman
Asali: Facebook

Matashiyar matar a lokacin da ta hadu da yaron wanda aikinsa ya kasance kiwon shanu sai ta tambaye shi idan zai so a sanya shi a makaranta, wanda ya amshi tayin.

Laylah ta nanata cewa ta hadu da danginsa kuma sun amince da bukatarta na rikon yaron bayan sun nuna turjiya.

Matar wacce ta cika da farin ciki ta wallafa hoton yaron tare da 'ya'yanta maza biyu.

Sakon nata ya zo kamar haka:

"Barka dai dangin FB, ku sadu da sabon dana Aliyu .. Na same shi a wuse2 yana zaune a karkashin wata inuwa, da alama ba ya jin dadi, wani ma'aikaci na ya tambaye shi abin da ke damunsa sai ya ce ya karya azuminsa ne saboda ba ya gani.

"..Shekararsa 12 kawai, aikinsa a kullum shi ne yawo da shanu da yawa daga wannan gefe zuwa wancan, na nemi ganawa da shi, ya shigo ya sace zuciyata, na tambaye shi ko yana son zuwa makaranta nan da nan ya ce eh, na nemi adireshin gidansa da lambar wayar mahaifinsa, wanda ya ba ni daidai, na kira su, muka yi ta kaiwa da komowa.

"... Dole sai da na tuka kaina sau da yawa don dangin su yarda, a karshe suka yarda.. lol. Don haka yanzu ga mu nan, Zai fara makaranta gobe insha Allah .. Yarana sun cika da murnar haduwa da shi . Yanzu haka ina da yara kyawawa guda 3 ... "

'Yan Najeriyar sun cika da yabon Laylah kuma suka yi kwararo mata ruwan addu'o'i.

KU KARANTA KUMA: Idanu sun zubda hawaye, Jalingo ta cika tankam yayin da aka yi jana'izar Mama Taraba

Zulkarnain Yabagi ya yi martani:

"Mun gode da irin alherin da kike nuna wa masu karamin karfi, da fatan Allah Ya sake cika maki aljihunki kuma ya albarkace ki a koyaushe."

Mihammad Jamil ya yi tsokaci:

"Masha Allah. Ke ta daban ce. Ubangiji zai saka maki da nikin ba-ninki.

"Ina fatan sauran mutane suyi koyi daga wannan alherin da kika yiwa wannan karamin yaron."

Kaka Hussaini Anthony ya ce:

“Ina alfahari da ke laylah, Allah ya biya ki. Ci gaba da yin kyakkyawan aikin."

A wani labarin, a ranar Litinin, 10 ga watan Mayu, 2021, Malam Salim Jafar Mahmud Adam ya bada sanarwar cewa Mai dakinsa ta haihu.

Legit.ng Hausa ta samu labari cewa wannan Bawan Allah ya samu baiwar ‘diya mace ne a daidai ranar 28 ga watan Ramadan, 1442.

A daidai lokacin da musulmai su ke shirin bankwana da watan Ramadan, sai aka ji Salim Jafar Adam ya samu karuwar namiji.

Asali: Legit.ng

Online view pixel