Da duminsa: Barayi sun kai hari Aso Rock, sun shiga gidan nakusa da Buhari

Da duminsa: Barayi sun kai hari Aso Rock, sun shiga gidan nakusa da Buhari

Labari da duminsa na nuna cewa wasu barayi sun yi yunkurin fadawa cikin gidan shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, dake Aso Rock, birnin tarayya Abuja.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki da yammacin Litinin.

Garba ya bayyana cewa barayin basu samu nasarar satan komai ba.

"Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, ya tabbatar da cewa an yi "wawan yunkurin" yi masa fashi a gidansa misalin karfe 3 na daren nan amma basu samu nasara ba," Garba Shehu yace.

"Farfesa Gambari...ya ce babu wani abin damuwa."

Da duminsa: Barayin sun kai hari fadar Aso Villa, sun shiga gidan nakusa da Buhari
Da duminsa: Barayin sun kai hari fadar Aso Villa, sun shiga gidan nakusa da Buhari Credit: @GazetteNGR
Asali: Twitter

Asali: Legit.ng

Online view pixel