Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Sanda Sun Kuɓutar Da Mutum 30 Cikin 40 Da Aka Sace Wurin Tahajjud a Katsina

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Sanda Sun Kuɓutar Da Mutum 30 Cikin 40 Da Aka Sace Wurin Tahajjud a Katsina

- Hukumar yan sandan jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarar kuɓutar da mutum 30 daga cikin waɗanda yan bindiga suka sace a wajen sallar tahajjud

- Kakakin yan sandan jihar SP Sambo Isa, yace sun sami wannan nasara ne da haɗin guiwar yan ƙato-da-gora da kuma wasu mutanen unguwar da lamarin ya faru

- Sai dai wasu daga cikin mutanen yankin sunce mutanen ne suka dawo gida da kansu ba yan sanda ne suka kuɓutar da su ba

Rundunar yan sandan jihar Katsina tace ta kuɓutar da mutane 30 daga cikin 40 da yan bindiga suka sace a wurin sallar tahajjud a wani masallaci dake ƙaramar hukumar Jibia, jihar Katsina.

KARANTA ANAN: Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11 a Sabon Hari Da Suka Kai Jihar Katsina

Rahotanni sun tabbatar cewa wasu yan bindiga sun yi awon gaba da masallata 40 a wani masallaci suna tsakar sallar tahajjud.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar, SP Gambo Isa, ya shaidawa BBC cewa wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun shiga unguwar Kwata ɗauke da makamai, suka kutsa kai cikin wani sabon masallaci kuma suka sace mutane 40 a daren ranar Litinin.

Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Sanda Sun Kuɓutar Da Mutum 30 Cikin 40 Da Aka Sace Wurin Tahajjud a Katsina
Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Sanda Sun Kuɓutar Da Mutum 30 Cikin 40 Da Aka Sace Wurin Tahajjud a Katsina Hoto: @shehusani
Asali: Twitter

Ita dai sallar Tahajjud ana gudanar da ita ne da tsakiyar dare, inda mutane ke haɗuwa a cikin masallaci su gudanar da sallar cikin jam'i.

Mai magana da yawun yan sandan yace: "Yayin da yan bindigan suka isa unguwar sai suka fara harbe-harbe a sama, sannan suka yi awon gaba da mutanen da suka fito yin sallar tahajjud."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Soji Sun Damƙe Mayaƙan Boko Haram 10 a Jihar Kano

"Bayan samun rahoton faruwar lamarin ne, jami'an tsaro tare da haɗin guiwar yan ƙato da gora da wasu mutanen gari suka bi sawun yan bindigan har suka sami nasarar kuɓutar da mutum 30."

"Binciken da muka yi bayan kuɓutar da mutanen ya nuna cewa har yanzun akwai sauran mutum 10 da ba'a san inda suke ba"

SP Gambo ya ƙara da cewa tuni waɗanda aka kuɓutar ɗin suka isa ga iyalansu, babu wanda ya samu rauni.

Sai-dai wasu daga cikin mazauna unguwar da lamarin ya faru sun bayyana cewa mutanen da kansu suka dawo ba yan sanda suka kuɓutar da su ba.

A wani labarin kuma Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe

Musulmi na farko da ya taɓa lashe zaɓen magajin garin Landan, Sadiq Khan, ya sake komawa kan kujerar sa a karo na biyu bayan kammala Zaɓe

Khan ya sake samun nasara ƙarƙashin jam'iyyar hamayya ta Labour da kashi 55.2% yayin da babban abokin takararsa keda kashi 44.8%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel