Gwamnan Ondo Zai Buɗe Sabon Masallaci Na Farko da Aka Gina a Cikin Gidan Gwamnatin Jiharsa

Gwamnan Ondo Zai Buɗe Sabon Masallaci Na Farko da Aka Gina a Cikin Gidan Gwamnatin Jiharsa

- Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, ya bayyana cewa zai ƙaddamar da sabon masallacin da ya gina a ranar 4 ga watan Yuni

- Gwamnan yace buɗe masallacin zai zama ɗaya daga cikin ayyukan da zaiyi alfahari dasu wajen bikin cikarsa kwanaki 100 a kan kujerar gwamna

- Ya ƙara da cewa gwamnatin sa ba zata nuna banbanci a tsakanin addinai ba, ya kuma yi kira ga mabiya addinan jihar da su zauna lafiya a tsakaninsu

Gwamnan jihar Ondo, Oluwarotimi Akeredolu, yace buɗe sabon masallaci a cikin gidan gwamnatin jihar ranar 4 ga watan Yuni zai zama ɗaya daga cikin ayyukan da zaiyi alfahari dasu a bikin cikarsa kwana 100 a kan mulki.

KARANTA ANAN: NDLEA Ta Bankado Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Ta Yanar Gizo, Ta Kama 5 a Abuja

Mr Akeredolu, wanda aka sake zaɓensa a karo na biyu, yace za'a sanya wa masallacin sunan tsohon shugaban hukumar kula da walwalar musulmai ta jihar, Khalid Fawehinmi, wanda ya rasu a shekarar 2020.

Gwamnan ya faɗi haka ne a ranar lahadi yayin da ya karɓi baƙuncin Shugabannin musulmai na jihar a wajen buɗe baki a ɗakin taro na ƙasa-da-ƙasa dake Akure.

Gwamna Zai Ƙaddamar da Masallaci Na Farko da Aka Gina a Cikin Gidan Gwamnatin Jiharsa
Gwamna Zai Ƙaddamar da Masallaci Na Farko da Aka Gina a Cikin Gidan Gwamnatin Jiharsa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Gwamnan yace: "Gwamnatin mu itace ta farko data gina masallaci a cikin gidan gwamnati, kuma ina mai tabbatar muku da cewa ba zan nuna banbanci a tsaƙanin addinai ba."

"Zamu sanya wa masallacin sunan tsohon shugaban hukumar kula da walwalar musulmai ta jihar, Khalid Fawehinmi,"

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Ƙona Ofishin Yan Sanda a Jihar Abia

"Ina kira ga mabiya addinin musulunci da kuma kiristanci da su zauna lafiya a tsakanin su, domin duka addinan biyu suna koyar da son juna da kuma sadaukarwa."

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa zata bada muhimmanci ga cancantar mutum bawai daga wane addini ya fito ba.

Shugaban hukumar kula da walwalar musulmai, Zikrullah Chandy, ya yabawa gwamnan bisa soyayyar da yake nunawa musulmai a faɗin jihar.

Ya kuma jinjinawa gwamnan bisa wannan namijin ƙoƙari da yayi na gina masallaci a cikin gidan gwamnati domin musulmai dake wajen su rinƙa ibada.

A wani labarin kuma Jami'an Soji Sun Damƙe Mayaƙan Boko Haram 10 a Jihar Kano

Sojoji sun yi ram da wasu mutane da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ta'addaci ta Boko Haram ne a cikin garin Kano ranar Asabar.

Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 10 ne suka shiga hannu lokacin da suka yi ƙoƙarin kai hari wani masallaci a yankin Hotoro.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel