Amaechi ya kafa kwamitin mutum 11 domin binciken Hadiza Bala Usman

Amaechi ya kafa kwamitin mutum 11 domin binciken Hadiza Bala Usman

- Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi, ya kafa kwamitin mutum 11 domin binciken Hadiza Bala Usman

- An dakatar da shugabar NPA ne sakamakon zarginta da ake da badakalar wasu kudade har N165 biliyan

- Duk da musantawar da tayi, Shugaban ayyukan da suka shafi teku, Suleiman Auwalu ne zai jagoranci kwamitin

Sakamakon zargin badakalar wasu kudade da ake yi kuma ya kai ga an dakatar da manajan daraktan hukumar kula da hanyoyin shige da fice na ruwan kasar nan (NPA) Hadiza Bala Usman, ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya kafa kwamitin mutum 11 domin bincikenta.

Vanguard ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman ne sakamakon zarginta da ake da kalmashe wasu rarar kudi har N165 biliyan inda ta ki saka su a asusun gwamnati, zargin da ta musanta.

Kwamitin mutum 11 ya samu shugabancin Suleiman Auwalu, darakta ne a bangaren da ya shafi teku, sai Gabriel Fan, mataimakin darakta a bangaren shari'a, ma'aikatar sufuri ta tarayya ce zata yi aiki a matsayin sakatariyar kwamitin.

KU KARANTA: Kano: Barkewar amai da gudawa ta janyo rasa rayuka 15, 40 suna asibiti kwance

Amaechi ya kafa kwamitin mutum 11 domin binciken Hadiza Bala Usman
Amaechi ya kafa kwamitin mutum 11 domin binciken Hadiza Bala Usman. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Buhari zai yi bikin sallah a fadar Aso Rock, yace baya bukatar gaisuwar sallah

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, a cikin kwanakin karshen mako ne hankulan jama'a suka tashi a Hotoro ta arewa dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano bayan sojoji sun cafke wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne.

Samamen da sojin suka kai a daren Asabar sun dira wani sabon gida ne da aka gano cewa jama'an daga jihar Borno suka tare.

Kamar yadda takardar da aka fitar ta bayyana, an tabbatar da kama mutum 13. Tun a farkon zuwan Boko Haram jihar Kano, Hotoro ce cibiyar ayyukansu kafin a tarwatsa su sakamakon kokarin jami'an tsaro da na mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel