Yadda aka yi amfani da kafar sada zumunta wurin fallasa Boko Haram a Kano

Yadda aka yi amfani da kafar sada zumunta wurin fallasa Boko Haram a Kano

- Hankulan jama'ar jihar Kano ya tashi bayan kama wasu mutum 13 da ake zargin 'yan Boko Haram ne a Hotoro

- Mazauna yankin sun tabbatar da cewa an fara gangami tare da sanarwar wanzuwar 'yan Boko Haram din ne a kafafen sada zumunta

- Yankin Hotoro zuwa Eastern bye-pass ya kasance dandali tare da mafakar jama'a daga Borno kuma suna ta gina gidaje a wurin

A cikin kwanakin karshen mako ne hankulan jama'a suka tashi a Hotoro ta arewa dake karamar hukumar Nasarawa ta jihar Kano bayan sojoji sun cafke wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne.

Samamen da sojin suka kai a daren Asabar sun dira wani sabon gida ne da aka gano cewa jama'an daga jihar Borno suka tare. Kamar yadda takardar da aka fitar ta bayyana, an tabbatar da kama mutum 13.

Tun a farkon zuwan Boko Haram jihar Kano, Hotoro ce cibiyar ayyukansu kafin a tarwatsa su sakamakon kokarin jami'an tsaro da na mazauna yankin, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Melaye: Buhari ya fito yayi mana magana, ba Garba Shehu ko Adesina muka zaba ba

Yadda aka yi amfani da kafar sada zumunta wurin fallasa Boko Haram a Kano
Yadda aka yi amfani da kafar sada zumunta wurin fallasa Boko Haram a Kano. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wasu 'yan Najeriyan basu tausayin kasarsu ko kadan, Shugaba Buhari

Kamar yadda wani mazaunin yankin mai suna Malam Muhammed Amadi ya sanar, sojojin sun yi aikin ne ba tare da jan hankalin jama'a ba.

Ya ce sojojin sun isa gidan wadanda ake zargin wurin karfe 9:15 na dare inda suka zagaye tare da yin awon gaba da wasu 'yan gidan.

Ya kara da cewa mutanen basu yi yunkurin gudu ko wani artabu da sojojin ba, hakan yasa ba a harba ko harsashi daya ba.

Aliyu Garba Hakimi wani mazaunin yankin ne kuma kamar yadda yace, ya fara jin wannan gangamin ne a kafafen sada zumunta.

Kamar yadda yace, bai san abinda yasa aka fara gangamin ba amma daga bisani ya gano cewa wasu irin mutane daga Borno sun cika yankin.

"Duk da basu da rigima, amma yadda suke basu son kowa ya zama wani abu daban. Gaskiya an fara gangamin ne kuma mutane da yawa sun fara zama cikin rashin yadda da su," yace.

A wani labari na daban, hargitsin cikin gida ya fara tsakanin mabiyan kungiyar Kwankwasiyya dake jihar Kano. Hakan ta faru ne sakamakon rabon kayan abinci na azumi na miliyoyin naira da wani yayi wa 'yan jam'iyyar a Kano.

Hadimin sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Sanusi Surajo, ya sanar da cewa ya ga wani bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta inda Dakta Adamu Dangwani ke shirin farraka kan 'yan Kwankwasiyyan.

Dangwani tsohon kwamishinan ruwa ne kuma shugaban ma'aikatan fadar gwamnatin Kano yayin mulkin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel