Da Ɗumi-Ɗumi: Jami'an Soji Sun Damƙe Mayaƙan Boko Haram 10 a Jihar Kano
- Sojoji sun yi ram da wasu mutane da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ta'addaci ta Boko Haram ne a cikin garin Kano ranar Asabar
- Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla mutane 10 ne suka shiga hannu lokacin da suka yi ƙoƙarin kai hari wani masallaci a yankin Hotoro
- Jami'an sojin sun ɗauke wasu abubuwa da basu yarda da su ba a kewayen masallacin kafin daga bisani su yi gaba da mutanen
Aƙalla mayaƙan ƙungiyar Boko Haram 10 ne suka shiga komar sojin Najeriya a jihar Kano, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Gwamnatin Tarayya Ta Yaba da Aikin NYSC, Tace Aikin Yayi Fice Wajen Haɗa Kan Yan Najeriya
Rahotanni sun bayyana cewa sojojin sun kama mutanen lokacin da suka kutsa Filin Lazio dake yankin Hotoro a cikin garin Kano da yammacin ranar Asabar.
Waɗanda aka kama ɗin sun yi koƙarin kai hari ne a wani masallaci da kuma wasu gidaje dake yankin, sai dai rahotanni sun nuna cewa farmakin yazo dai-dai lokacin da musulmai ke shan ruwa bayan sun kai azumi.
Wannan lamarin dai ya sanya tsoro sosai a zukatan mazauna yankin.
KARANTA ANAN: Aljanu Biliyan 3 su ka karbi Darikar Tijjaniya a Duniya inji Sheikh Dahiru Bauchi
An gano cewa masallacin da suka yi kokarin kai harin mallakin wasu mutane yan asalin jihar Borno ne, waɗanda suka baro gidajensu saboda rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a arewa maso gabas.
Hakanan kuma, An gano cewa jami'an sojin, sun tattara wasu abubuwa da ba'a gane su ba a kewayen masallacin.
Da aka tuntuɓi mai magana da yawun rundunar sojoji, Mohammed Yerima, yayi alƙwarin yiwa manema labarai bayani ranar Lahadi.
A wani labarin kuma Ortom Ya Yiwa El-Rufai Wankin Babban Bargo, Ya Ce Yana Daya Daga Cikin Makiyan Najeriya Na Hakika
Gwamna Samuel Ortom ya bayyana takwaransa na jihar Kaduna a matsayin makiyin Najeriya.
Gwamnan na Benuwai ya kuma bayyana cewa Malam Nasir El-Rufai na daya daga cikin wadanda ke yaudarar Shugaba Buhari.
Asali: Legit.ng