Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11 a Sabon Hari Da Suka Kai Jihar Katsina
- Wasu yan bindiga sun kai hari a garin Tsatskiya dake ƙaramar hukumar Safana, jihar Katsina inda suka hallaka mutum 11 tare da jikkata wasu da dama
- Maharan sun isa garin ne da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar Ranar Asabar domin ɗaukar fansa a kan kisan da mutanen garin suka yi wa ɗan leƙen asirinsu
- Rahotanni sun bayyana cewa kwana huɗu kafin harin mazauna garin sun gano wani ɗan leƙen asiri dake aiki da yan bindiga kuma suka kashe shi
Aƙalla mutane 11 wasu yan bindiga suka hallaka yayin da mutum uku suka samu raunuka a garin Tsatskiya dake ƙaramar hukumar Safana, jihar Katsina.
KARANTA ANAN: Da Duminsa: ’Yan Bindiga Sun Kashe Jigo a Kaduna, Matarsa da Sirikarsa
An garzaya da Mutane uku da suka sami raunuka asibitin Dutsin-ma domin samun kulawa ta musamman.
Rahoton Dailytrust ya bayyana cewa maharan sun farmaki garin ne da misalin ƙarfe 9:30 na safiyar ranar Asabar.
Ana zargin dai maharan sun kawo harin ne domin ɗaukar fansa bisa kisan da mazauna garin suka yiwa ɗan leƙen asirin su.
Kwanaki huɗu kafin kawo harin, mutanen garin sun gano wani ɗan leƙen asiri dake aiki da yan bindiga suka kashe shi.
KARANTA ANAN: NDLEA Ta Bankado Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Ta Yanar Gizo, Ta Kama 5 a Abuja
Wata majiya ta bayyana cewa yan bindigar sun isa garin ne a kan mashina, inda suka buɗe wuta kan me uwa da wabi wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 11.
Mutanen garin Tsatskiya sun kwarara zuwa Dutsin-ma domin tseratar da rayuwarsu.
Kakakin hukumar yan sandan jihar Katsina ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya musanta adadin da ake yaɗawa cewa mutum 11 ne suka rasa rayukansu.
Yace: "Mun samu rahoton kai hari ƙauyen Tsatskiya kuma mutane uku ne suka rasa rayukansu ba 11 ba kamar yadda ake yaɗawa."
A wani.labarin kuma Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe
Musulmi na farko da ya taɓa lashe zaɓen magajin garin Landan, Sadiq Khan, ya sake komawa kan kujerar sa a karo na biyu bayan kammala Zaɓe.
Khan ya sake samun nasara ƙarƙashin jam'iyyar hamayya ta Labour da kashi 55.2% yayin da babban abokin takararsa keda kashi 44.8%.
Asali: Legit.ng