Da duminsa: An sheke jami'an 'yan sanda 6 yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki ofishin 'yan sanda

Da duminsa: An sheke jami'an 'yan sanda 6 yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki ofishin 'yan sanda

- 'Yan bindiga da suke kaiwa 'yan sanda da ofisoshinsu hari sun sauya salo a inda suka koma yankin kudu-kudu na kasar nan

- A cikin sa'o'i kadan, an kaiwa ofishin 'yan sanda hari kuma an kashe jami'ai a jihohin Ribas da na Akwa Ibom

- Yayin da ake tunanin 'yan sanda 7 sun mutu a harin Ribas, an kashe wasu jami'ai shida a harin da aka kai Akwa Ibom

'Yan bindiga da ake zargin mambobin IPOB ne sun kai mugun farmaki ofishin 'yan sanda dake Odoro Ikpe a karamar hukumar Ini ta jihar Akwa Ibom.

Jami'ai shida sun rasa rayukansu a harin da aka kai a sa'o'in farko na ranar Asabar, 8 ga watan Mayu, The Punch ta ruwaito haka.

KU KARANTA: Sanata ya bukaci majalisa ta dauka tsatsauran mataki a kan mulkin Buhari

Da duminsa: An sheke jami'an 'yan sanda 6 yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki ofishin 'yan sanda
Da duminsa: An sheke jami'an 'yan sanda 6 yayin da 'yan bindiga suka kai farmaki ofishin 'yan sanda. Hoto daga @daily_trust
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Melaye: Buhari ya fito yayi mana magana, ba Garba Shehu ko Adesina muka zaba ba

Hakazalika, a yayin bada rahoton harin, The Cable ta ce wannan ne karo na biyu da ake kai hari cikin mako daya a jihar ta kudu.

Legit.ng ta tabbatar da cewa wannan harin ya zo ne yayin da ake ta kai hare-hare ofishin 'yan sanda a yankin.

Hare-haren 'yan bindiga ya zama ruwan dare domin kuwa ba a yin kwanaki kalilan ba tare da sun kai mugun hari ba. Suna kone ofishin 'yan sanda tare da kashe jami'ai.

Duk da ana zargin mambobin IPOB da kai miyagun hare-hare, su kan musanta hakan.

A wani labari na daban, kasa da sa'o'i 24 da nada sabon kwamishinan 'yan sanda a jihar Anambra, Christopher Adetokumbo Owolabi, 'yan bindiga sun kai farmaki ofishin 'yan sanda dake Obosi a karamar hukumar Idemili a jihar inda suka sheke 'yan sanda biyu.

'Yan bindigan sun kai farmaki ofishin 'yan sandan a yammacin Laraba inda suka saki dukkan masu laifi dake ofishin sannan suka banka masa wuta, Daily Trust ta wallafa.

Wata majiya mai kusanci da ofishin 'yan sandan tace 'yan bindiga sun isa da yawansu kuma sun kai hari ofishin wurin karfe 11 na dare. Ya bayyana sunayen jami'an da Sifeta James da Awalu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel