Wasu 'yan Najeriyan basu tausayin kasarsu ko kadan, Shugaba Buhari

Wasu 'yan Najeriyan basu tausayin kasarsu ko kadan, Shugaba Buhari

- Shugaba Buhari ya koka da yadda wasu 'yan Najeriya basu tausayawa kasar su kwata-kwata

- Shugaban kasan yace kowacce doka ya saka domin amfanin 'yan kasa sai an karya ta

- Ya jajanta yadda ya rufe iyakokin kasar nan amma ake samun hanyar shigowa da makamai

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta abinda ya kwatanta da 'rashin tausayin wasu 'yan Najeriya' ga cigaba, inda yayi kira ga 'yan kasa da su dinga dubawa kasar nan.

Buhari ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da yake jin bayani daga PEAC wacce Farfesa Doyin Salami ke jagoranta, a taronta na 6 a gidan gwamnati dake Abuja.

Ya koka da yadda wasu miyagun mutane marasa kishin kasa ke zagon kasa ga duk dokokin gwamnati koda kuwa an yi su ne domin amfanin kasar nan, The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sake kwashe daliban jami'a da ba a san yawansu ba

Wasu 'yan Najeriyan basu tausayin kasarsu ko kadan, Shugaba Buhari
Wasu 'yan Najeriyan basu tausayin kasarsu ko kadan, Shugaba Buhari. Hoto daga @TheCableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Gara mu rasa rayukanmu da a tsige Buhari daga kujerarsa, Masoyan shugaban kasa

Kamar yadda takardar da mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasan a fannin yada labarai, Femi Adesina ya fitar, Buhari yace duk da rufe iyakokin kasar nan da yayi na sama da shekara daya, wasu 'yan Najeriya sun samu hanyar shigo da kayan da bai dace ba.

"Wasu mutane basu tausayin kasar nan," shugaban kasa yace.

"Mun rufe iyakokin kasar nan domin hana shigo da kayayyakin man fetur da makamai.

“A wannan lokacin ne shugaban hukumar kwastam ya kira ni yake fada min sun kwace tanka 40 dankare da fetur. A take nace a siyar da man, a siyar da motocin kuma a saka kudin a asusun kasa.

"Sun cigaba da siyo makamai su shigo da su kasar nan, suna siyo shinkafa da sauransu. Nace a harbe duk wanda aka kama dauke da AK47 ba bisa ka'ida ba, amma sun ki denawa. Dole ne jama'a su nuna kishin kasar su," yace.

A wani labari na daban, Sanata mai wakiltar Osun ta gabas, Francis Fadahunsi, yayi kira ga majalisar dattawa da ta dauka mummunan mataki domin kawo karshen kalubalen tsaro da ya addabi kasar nan.

Tuni dai yace "Majalisa na da karfin ikon nadawa ko tsigewa", kuma akwai bukatar majalisar dattawa tayi wani abu idan matsalar tsaron kasar nan bata inganta ba.

Kamar yadda wani bidiyonsa ya nuna a ranar Laraba, dan majalisar karkashin jam'iyyar PDP, yayi jawabi yayin da yake bada gudumawa a wata tattaunawa a kan tsaro a zauren majalisar, The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel