Wasu Yan Bindiga Sun Ƙone Ofishin Jami’an Tsaro da Motarsu, Sun Hallaka Mutum Biyar
- Aƙalla mutum biyar ne Suka rasa rayukansu a wani sabon hari da yan bindiga suka kai Ƙauyen Izubulu dake cikin jihar Anambra
- Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan sun ƙona ofishin jami'an tsaron sa kai da motar hawan su
- Kakakin hukumar yan sandan jihar ya tabbatar da kai harin amma yace bashi da cikakken bayani kan mutum nawa harin ya shafa
Mutum biyar sun rasa rayukansu lokacin da wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba suka kai hari ƙauyen Ozubulu dake ƙaramar hukumar Ekwusigo a jihar Anambra ranar Lahadi da daddare.
KARANTA ANAN: Wasu Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 11 a Sabon Hari Da Suka Kai Jihar Katsina
Ƴan bindigan sun ƙone ofishin jami'an tsaron sa kai wato Vigilanti da abun hawansu, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
Daga cikin waɗanda aka kashe a yayin harin akwai wani sanannen ɗan kasuwa ɗan asalin ƙauyen, yayin da sauran mamatan ba'a gano bayanan su ba.
Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar ta Anambra, PPRO, Mr. Ikenga Tochukwu, ya tabbatar da kai harin a ƙauyen Ozubulu.
Sai-dai kakakin yan sandan ya ƙara da cewa ba'a bashi cikakken bayanin mutanen da harin ya ritsa da su ba.
KARANTA ANAN: Musulmi Ya Sake Ɗarewa Kujerar Magajin Garin Landan Bayan Lashe Zaɓe
Mr. Tochukwu yace: "Eh, mun samu rahoton an kai hari a ƙauyen Izubulu, amma ba ofishin yan sanda bane abun ya shafa, a ofishin yan Vigilanti ne na yankin."
"Yan bindigan sun kai hari ofishin ne a cikin motar Sienna da kuma kan mashina. Mun tura jami'an tsaro zuwa yankin kuma komai yafara komawa yadda yake a baya."
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa idonsa ya gano masa gawarwakin mutum biyar kwance a wurin da lamarin ya faru.
A cewar mutumin, maharan sun zo da yawa kuma suna isowa suka fara harbi kan me uwa da wabi.
A wani labarin kuma NDLEA Ta Bankado Masu Safarar Miyagun Kwayoyi Ta Yanar Gizo, Ta Kama 5 a Abuja
Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta bankaɗo wasu gurɓatattun mutane dake safarar ƙwayoyi a yanar gizo.
A binciken da NDLEA tayi ta samu nasarar cafke mutane biyar a babban birnin tarayya Abuja ta hanyar ɗana musu tarko da siyan kayan su a yanar gizo.
Asali: Legit.ng