Sheikh Gumi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan 'Yan Bindiga Suka Sace Dansa

Sheikh Gumi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan 'Yan Bindiga Suka Sace Dansa

- Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana dalilin da ya sa ya bayar da fatawar cewa a biya diyya ga 'yan fashi don sakin wadanda suka kama

- Malamin ya tausaya wa iyayen da 'yan fashi suka sace' ya'yansu

- 'Yan bindiga sun mamaye wasu yankunan Arewacin Najeriya

Wani fitaccen mai wa’azin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya bayyana cewa zai je fadar Aso Rock idan ‘yan fashi suka sace dansa.

Malamin ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake zantawa da BBC Pidgin wanda aka buga a ranar Juma’a, 7 ga Mayu.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Shahararren malamin Musulunci ya yi rashi na matarsa

Sheikh Gumi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan 'Yan Bindiga Suka Sace Dansa
Sheikh Gumi Ya Bayyana Abin Da Zai Yi Idan 'Yan Bindiga Suka Sace Dansa Hoto: Dr Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

Gumi ya bayyana cewa ba zai taba yin shiru ba idan yaronsa yana cikin daliban jami'ar Greenfield da aka sace.

Ya sake nanata shawarar da ya ba gwamnatin tarayya na ta biya Naira miliyan 100 kudin fansa don sakin daliban.

Malamin ya ce:

“Rayuwa da abu; haka za ku dube shi. Babban hakki ne akan gwamnati ta kare rayuka. Yanzu muna da rayukan mutane ko kuma miliyan N100 a cikin hatsari kuma rayukan matasa 17 da basu ji ba basu gani ba.

"Da ace ɗana yana wurin. Ba zan iya yin shiru ba. Zan je in kwankwasa Aso Rock, idan ɗana yana wurin. Su ma 'ya'yana ne."

Ya ce ‘yan fashi ba sa jin zafin satar mutane saboda ba su da ingantaccen ilimi.

KU KARANTA KUMA: Na Kaɗu Matuƙa Da Samun Labarin Mutuwar Aisha Alhassan, Atiku

Gumi ya ce ya sanar da gwamnati cewa idan ‘yan fashi suna da makarantu, ba za su afkawa mutane ba.

A gefe guda, fitattun ‘yan Najeriya wadanda ke daukar nauyin ta’addanci za su fuskanci tsarin shari’a nan ba da jimawa ba kasancewar gwamnatin tarayya ta kammala shirye-shiryen gurfanar da su.

Babban Atoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami (SAN) ne ya bayyana wannan ci gaban a ranar Juma'a, 7 ga watan Mayu, jaridar Punch ta ruwaito.

Malami wanda bai bayyana sunayen wadanda ake zargin ba ko kuma yawan mutanen da abin ya shafa ba ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban Kasa a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, in ji jaridar The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel