Da duminsa: Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus Yayin da Motar Bas Ta Kama Wuta a Kan Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan

Da duminsa: Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus Yayin da Motar Bas Ta Kama Wuta a Kan Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan

- Hatsarin mota ya cika da wasu fasinjoji 14 inda suka kone kurmus

- Lamarin ya afku ne a daren ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu, a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan

- Kakakin hukumar kiyaye haddura (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da afkuwar hatsarin

Fasinjoji 14, ciki har da yara uku, sun kone kurmus a wani hadari da ya faru a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hadarin wanda ya faru da misalin karfe 10:20 na daren ranar Alhamis ya cika da wata mota kirar Toyota RAV 4 kalar azurfa mai lamba, LND 13 GS; motar Toyota Camry mai lamba, GGE 369 GJ da kuma wata motar bas kirar Mazda da ba a san lambarta ba.

An tattaro cewa wata motar bas ta kasuwa da ta sha gaban wata mota ba bisa ka'ida ba ta bugi wata batacciyar mota kirar Toyota Rav 4 da aka ajiye a tsakiyar hanya.

Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus Yayin da Motar Bas Ta Kama Wuta a Kan Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan
Fasinjoji 14 Sun Kone Kurmus Yayin da Motar Bas Ta Kama Wuta a Kan Babbar Hanyar Legas Zuwa Ibadan Hoto: Olukayode Jaiyeola
Asali: Getty Images

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: Jami'an Tsaro sun dakile sabon hari da aka kaiwa Ofishin ‘yan sanda na Imo, sun kashe yan daba 8

An ce motar bas din ta kwacewa direbanta sannan kuma ta kife sau da dama kafin ta kama da wuta.

Kakakin hukumar kiyaye haddura (TRACE), Babatunde Akinbiyi, ya tabbatar da afkuwar hatsarin a safiyar ranar Juma’a.

Akinbiyi ya ce fasinjoji 14 ciki har da yara uku aka tabbatar da sun kone kurmus “a cikin mummunar hatsarin motar.

"Gaba daya, fasinjoji 17 na cikin bas din lokacin da hatsarin ya faru, tare da uku da suka ji munanan raunuka, kuma 14 sun kone fiye da yadda za a iya gane su, daga cikinsu akwai yara uku," in ji shi.

Ya ce jami'an kungiyar ta TRACE da sauran jami'an tsaro sun garzaya da mutum biyu da lamarin ya rutsa da su zuwa Asibitin Gaggawa na Jihar Legas da kuma daya zuwa Babban Asibitin, Gbagada, Legas.

KU KARANTA KUMA: Jita-Jitan Hare-Haren Yan Bindiga Ya Kawo Hargitsi a Abuja Yayin da Iyaye Ke Janye Yara Daga Makarantu

A halin yanzu, TRACE ta tausaya wa dangin wadanda suka mutu, tana mai gargadin direbobi da “su guji gudu da, wuce gona da iri da dabi’un da ke jefa sauran masu amfani da hanyar cikin hadari”.

A wani labarin, an shiga zaman ɗar-ɗar a Ogba, jihar Legas kan zargin harbe wani ɗan acaɓa da wani ɗan sanda ya yi.

Wata majiya ta shaidawa The Punch cewa rikicin ya fara ne tun juya a lokacin da ɗan sandan ya ƙi biyan ɗan acaɓan kudin ɗaukansa da ya yi.

Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta shaidawa majiyar Legit.ng cewa an kashe mutum biyu a daren jiya Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng