Hada Layin Waya da NIN Zai Taimaka Wajen Magance Matsalolin Tsaro, Buhari

Hada Layin Waya da NIN Zai Taimaka Wajen Magance Matsalolin Tsaro, Buhari

- Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yace haɗa layukan waya da NIN zai taimaka wa gwamnati wajen yaƙin da take da matsalar tsaro a ƙasar nan

- Buhari yayi kira ga yan Najeriya dama waɗanda doka ta basu damar zama a ƙasar nan da su gaggauta mallakar lambar NIN

- Yace tsarin haɗa layin waya da NIN zai sa gwamnati ta samu ainihin bayanan kowanne ɗan ƙasa

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, yace aikin dake gudana na haɗa layukan waya da lambar ɗan ƙasa NIN a faɗin ƙasar nan zai taimaka matuƙa wajen zaƙulo ainihin bayanan mutane, ciki kuwa harda yan damfara.

KARANTA ANAN: Kungiyar Ƙwadugo Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Karta Kuskura Ta Zabtarewa Ma’aikata Albashi

Shugaban ya kuma roƙi yan Najeriya dasu bada haɗin kai wajen gudanar da aikin, wanda a cewarsa zai samar da tsari mafi sauƙi wajen dawo da zaman lafiya da cigaban tattalin arziƙi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Shugaba Buhari yayi wannan jawabi ne yayin da yake ƙaddamar da shirin haɓɓaka ƙirƙirar yan asalin ƙasa a fannin sadarwar Najeriya da kuma sabon tsarin samar da NIN a fadarsa dake Abuja.

NIN-SIM: Haɗa Layin Waya Da NIN Zai Taimaka Mana Wajen Magance Matsalar Tsaro, Buhari
NIN-SIM: Haɗa Layin Waya Da NIN Zai Taimaka Mana Wajen Magance Matsalar Tsaro, Buhari Hoto: @FMoCDENigeria
Asali: Twitter

Buhari ya ƙara da cewa idan har za'a sami ainihin bayanai na gaba ɗaya yan Najeriya da waɗanda doka ta basu ikon zama a ƙasa. Kuma a rinƙa samun bayanai akansu yadda ya kamata, hakan zai taimaka wajen daƙile matsalar tsaro.

KARANTA ANAN: Wata Mummunar Gobara Ta Laƙume Gidaje 100 a Jihar Taraba, Mutum Biyu Sun Rigamu Gidan Gaskiya

Shugaba Buhari yace:

"NIN zata cike mana gurbin ɗaya daga cikin raunin mu a ɓangaren tsaro. Zamu samu dama cikin sauki mu gano kowanne ɗan Najeriya, zamu gane mutane cikin sauki, ciki kuwa harda yan damfara."

"Lambar NIN itace tushen bayanan yan ƙasa; Duk yan asalin ƙasa dama waɗanda doka ta basu izinin zama muna umartar su suje su mallaki NIN. Zata bada damar sanin ayyukan gwamnati kuma gwamnati zata sami ainihin bayanan da take buƙata wajen gudanar da ayyukanta ta hanya mafi sauƙi.

Shugaban ya ƙara da cewa kaddamar da wannan shiri na tsari da kuma manufar rijistar layin waya yazo a lokacin da ya dace, domin zai taimaka wajen ƙoƙarin da gwamnati take na dawo da zaman lafiya da kuma farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasa.

A wani labarin kuma Dalilin da Yasa Har Yanzun Hukumar DSS Bata Damƙe Sheikh Gumi Ba, Tsohon Darakta

Tsohon daraktan hukumar tsaro DSS yace yana da matuƙar wahala hukumar ta iya yanke hukuncin kama malamin addinin musulunci, Ahmad Gumi.

Tsohon daraktan ya bayyana dalilinsa da cewa idan ka kama shi a yanzun to zaka tsokalo masu goyon bayansa ne ko kuma waɗanda yake wa aiki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262