Kungiyar Ƙwadugo Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Karta Kuskura Ta Zabtarewa Ma’aikata Albashi

Kungiyar Ƙwadugo Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Karta Kuskura Ta Zabtarewa Ma’aikata Albashi

- Ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa, NLC, ta gargaɗi gwamnatin tarayya da kada ta kuskura ta zabtarewa ma'aikata albashinsu

- Shugaban NLC, Ayuba Waba, shine ya bayyana haka yayin da yake martani kan kalaman da ministan Kuɗi, Zainab Ahmed, tayi

- Waba yayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya dawo da ministan kuɗin kan hanya tun kafin ta jawo wata matsala a Najeriya

Ƙungiyar ƙwadugo ta ƙasa (NLC) a ranar Laraba ta gargaɗi gwamnatin tarayya da ta dakatar da shirinta na zabtarewa ma'aikata albashi, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Har Yanzun Hukumar DSS Bata Damƙe Sheikh Gumi Ba, Tsohon Darakta

NLC tace wannan shirin babban "kisan kai" ne ga ma'aikatan dake faɗin ƙasar nan.

Ministar Kuɗi, Zainab Ahmed, itace ta bayyana shirin gwamnatin a wajen wani taro ranar Talata, tace gwamnatin tarayya ta fara shirin rage yawan kuɗaɗen da take kashewa ta hanyar zabtarewa ma'aikata albashinsu.

Kungiyar Ƙwadugo Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Karta Kuskura Ta Zabtarewa Ma’aikata Albashi
Kungiyar Ƙwadugo Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Karta Kuskura Ta Zabtarewa Ma’aikata Albashi Hoto: news.neca.org.ng
Asali: UGC

Rahotanni sun nuna cewa, Zainab Ahmed ta umarci hukumar kula da albashi da kuɗaɗen shiga na ƙasa (NSIWC) tayi gaggawar sake duba albashin ma'aikata da kuma adadin hukumomin da gwamnatin ke dasu.

Amma a martanin da shugaban NLC, Ayuba Waba yayi, ya kira yi gwamnatin da karta kuskura ta taɓa mafi ƙarancin albashi na N30,000.

Yace kuɗin albashi da kuma alawus-alawus ɗin manyan masu riƙe da muƙaman gwamnati kaɗai yakamata gwamnatin ta rage.

Shugaban NLC yace:

"Wannan abu ne da bamu taɓa tunani ba cewa gwamnati na ƙoƙarin ta zabtarewa ma'aikata albashi a wannan lokacin da muke ciki, tambayar itace wane albashi gwamnatin take shirin zabtarewa?"

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Majalisa Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Dakatar da Shirin Ƙidaya 2021

"Bazai yuwu dai ace harda mafi ƙarancin albashi na N30,000 ba wanda a yanzun bazai iya siyan buhun shinkafa ɗaya ba. Ina fatan dai wannan shirin ba wata manufa bace a kan mafi ƙarancin albashin wanda har yanzun gwamnatocin jihohi ke jan ƙafa wajen fara aiki dashi."

"Abu ne da kowa ya sani cewa faɗuwar darajar Naira a ɗan kankanin lokaci ya rage darajar albashin da ma'aikatan ƙasar nan ke samu."

"Saboda haka wannan abin tsoro ne ace minista a gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata zabtare albashin ma'aikata a dai-dai wannan lokacin." inji shi

Shugaban ƙungiyar ƙwadugon yace ma'aikatan Najeriya na buƙatar ministan kuɗi, Zainab Ahmed, ta janye wannan shirin kuma ta baiwa ma'aikatan hakuri.

Ya kuma yi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya dawo da ministan kuɗin kan hanya kafin ta jawo matsala a Najeriya da kalamanta.

A wani labarin kuma Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi

Sheikh Gumi yayi kira ga gwamnati da kada ta ɗauki lamarin barazanar yan bindigan da suka yi garkuwa da ɗaliban jami'ar Greenfield da sauki.

A cewar shehin Malamin, kuɗin da suka nema suna da matuƙar yawa kuma gwamnati zata iya amfani da kuɗin a kama su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel