FG Ta Musanta Zargin Zata Zabtarewa Ma’aikata Albashi, Ta Bayyana Abinda Take Shirin Yiwa Ma’aikatan

FG Ta Musanta Zargin Zata Zabtarewa Ma’aikata Albashi, Ta Bayyana Abinda Take Shirin Yiwa Ma’aikatan

- Gwamnatin tarayya ta musanta zargin da ake mata cewa tana shirin zabtare albashin ma'aikatanta saboda ta rage wa kanta yawan kashe kuɗi

- Ministan kuɗi, Zainab Ahmed ce ta musanta zargin a wani jawabi data fitar ta hannun mai taimaka mata a fannin yaɗa labarai, Yunusa Tanko Abdullahi

- Ministan tace gwamnati na shirin gudanar da dai-daito a albashin ma'aikatanta, bayan gano wasu na amsar albashi fiye da wasu waɗanda suke matakin aiki iri ɗaya

Ministar kuɗi, Zainab Ahmed, ta musanta zargin dake cewa gwamnatin tarayya na shirye-shiryen zabtare albashin ma'aikatu, da hukumomin gwamnati, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wata Mummunar Gobara Ta Laƙume Gidaje 100 a Jihar Taraba, Mutum Biyu Sun Rigamu Gidan Gaskiya

A wani jawabi da mai baiwa ministan shawara kan harkokin yaɗa labarai, Yunusa Tanko-Abdullahi, ya fitar, Mrs. Ahmed tace gwamnati bata da niyyar zabtare alabashin ma'aikata sai dai tana shirin gudanar da dai-daito a tsakanin ma'aikatan.

FG Ta Musanta Zargin Zata Zabtarewa Ma’aikata Albashi, Ta Bayyana Abinda Take Shirin Yiwa Ma’aikatan
FG Ta Musanta Zargin Zata Zabtarewa Ma’aikata Albashi, Ta Bayyana Abinda Take Shirin Yiwa Ma’aikatan Hoto: @Zshamsuna
Asali: Twitter

Tace: "Mun gano cewa akwai wasu hukumomin gwamnati dake biyan ma'aikata albashi sama da yadda ake biyan wasu ma'aikatan daban da suke a matakin aiki ɗaya."

"Abinda gwamnati ke fatan yi shine gyara da kuma dai-daito a tsakanin dukkan ma'aikatan hukumominta. Muna son mu maida tsarin albashin hukumomin gwamnati ya zama iri ɗaya kuma cikin adalci."

"Abinda muke so kuma muke fata shine muyi adalci, da kuma dai-daito tsakanin ma'aikatan, kuma mu rage wa gwamnati kashe kuɗi."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sace Mutum 100 a Jihar Neja

Mrs Ahmed ta kara da cewa da zaran an kammala wannan aikin, kowane ma'aikacin gwamnati zai samu albashin sa dai-dai da kowane ma'aikaci da yake mataki ɗaya dashi a kowacce ma'aikata.

Tace: "Zamu yi wannan aikin gyaran ne saboda munga yawan kashe kuɗin da gwamnati ke yi ya ƙaru, kusan ya ninka biyu har ya zarta kuɗin da harajin da gwamnati ke samu."

A wani labarin kuma Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kareshi

Sanata Rochas Okorocha yace shugaba Buhari yana bashi tausayi saboda shi kadai ne yake ƙoƙarin gyara ƙasar nan.

Okorocha yace gaba ɗaya ministoci, daraktoci da dukkan na kusa da shugaban sun yi gum da bakinsu basa cewa komai wajen kare shugaban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel