Mutanen Unguwa a Kano Sun Takawa Masu Garkuwa da Mutane Birki
- Mazauna Unguwar Yamadawa a Kano sun dakile yunkurin garkuwa da wani mazunin yankin
- Wani shaidar gani da ido yace yan bindigar sun yi harbe harbe a iska bayan wanda suka zo dauka ya kubuce
- Hukumar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa suna fadada bincike
Wasu mazauna Unguwar Yamadawa a Dorayi Babba dake kwaryar birnin Kano sun kama wasu yan bindiga biyu da daren ranar Laraba bayan yunkurin su na satar mutane ya gaza cimma nasara.
Wani shaidar gani da ido ya shaidawa jaridar The Punch cewa yan bindigar sun shigo unguwar ne don yin garkuwa da wani magidanci lokacin da yake kokarin shiga gida da yamma bayan dawowar sa gidan.
DUBA WANNAN: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba
Wani wanda shaidar gani da ido ya ce, da ya tabbatar da abin da yake zargi, wanda aka zo garkuwa da shi yayi wa yan bindigar wayo ya shiga cikin wasu mutane.
Ya bayyana cewa tserewar wanda aka zo daukewar ya janyo harbe harbe don tsorata makwabta.
An ruwaito cewa mazauna yankin sun samu kwarin gwiwar fitowa tare da yiwa wanda ake zargin tara tara a babura lokacin da suke kokarin tserewa."
KU KARANTA: Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa
Yan bindigar, wanda aka kama, an mika su hannun yan sandan da suka zo yankin lokacin rikicin.
Da ake jin ta bakin sa, kakakin hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar, DSP Haruna Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin ya kuma ce suna ci gaba da bincike.
A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.
Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.
Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.
Asali: Legit.ng