Nasara daga Allah: Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga a yankunan Kaduna

Nasara daga Allah: Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga a yankunan Kaduna

- Dakarun sojin saman Najeriya sun ragargaji wasu gungun 'yan bindiga a wasu sassan jihar Kaduna

- An gano cewa miyagun sun tattaru wuri daya inda suke tattauna yadda zasu kai hari a garuruwan jihar

- Babu kakkautawa bayan samun bayanan sirri, dakarun sun yi musu ruwan wuta inda suka rage mugun iri

Gwamnatin jihar Kaduna tace dakarun sojin Najeriya sun halaka wata kungiyar 'yan bindiga dake jihar.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, wanda ya bayyana hakan a ranar Juma'a, yace 'yan bindigan sun tattaru ne domin kaddamar da wani hari a karamar hukumar Birnin Gwari.

Kamar yadda yace, dakarun sojin saman rundunar Operation Thunder Strike sun fada aiki kuma sun kawar da 'yan bindigan a yankin.

KU KARANTA: Juyin mulki: Hedkwatar tsaro ta ja kunnen sojoji da 'yan siyasa da kakkausar murya

Nasara daga Allah: Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga a yankunan Kaduna
Nasara daga Allah: Sojin saman Najeriya sun ragargaji 'yan bindiga a yankunan Kaduna. Hoto daga @DefensInfoNG
Asali: UGC

KU KARANTA: Da duminsa: Majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaro da IGP

"A yayin martani ga bayanan sirrin da dakarun sojin saman Najeriya suka samu, sun sheke wasu gungun 'yan bindiga da suka taru domin kaddamar da hare-hare a Birnin Gwari a ranar Litinin, 3 ga watan Mayun 2021," kwamishinan yace.

"Ma'aikatar tsaron cikin gida a ranar Lahadi 2 ga watan Mayun 2021 ta samu bayanin cewa 'yan bindiga sun tattaru a yankin Kugu dake Birnin Gwari wanda yake kusa da wasu kauyukan Shiroro na jihar Neja.

“Bayan samun rahoton wanda dakarun soji da sauran hukumomin tsaro suka tabbatar, OPTS sun fara aiki.

"Farmakin farko shine wanda sojojin suka kai babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari, Koriga, Polewire, Gagafada, Manini, Udawa, Labi, Buruku da sauran yankunan. Sun ragargaza 'yan bindigan a kauyen Kugu.

A farmaki na biyu, dakarun sun je hanyar Kaduna zuwa Abuja, Olam Company, Rugu, Akilbu, Polewire, Rijana, Kateri da Jere. An gano cewa ababen hawa sun koma wucewa lafiya kalau."

Kwamishinan yace Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, yayi godiya ga dakarun tare da dukkan cibiyoyin da suka bada gudunmawa.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana kaunar matasa kuma tana son ganinsu a cikin harkar shugabanci.

Gwamnan yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na kauna kuma yana fifita matasa a kasar nan inda ya kara da cewa hakan alama ce dake nuna goyon bayansa ga bukatar baiwa matasa mulki.

A watan Mayun 2018 shugaban kasan yasa hannu a kan kudirin rage shekarun takarar majalisar jiha da majalisar wakilai daga 30 zuwa 25, majalisar dattawa da gwamnoni daga 35 zuwa 30 da kuma kujerar shugaban kasa daga 40 zuwa 35.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel