Da duminsa: Mabiyan Father Mbaka sun fito zanga-zanga bayan bacewarsa a Enugu

Da duminsa: Mabiyan Father Mbaka sun fito zanga-zanga bayan bacewarsa a Enugu

- Jama'a mabiyan father Mbaka dake jihar Enugu sun fita zanga-zangar neman inda babban malamin yake

- An yi da shi zai halarci wani taron addu'o'i da za a yi a ranar Laraba da safe amma shiru kake ji babu labarinsa

- Duk da rahotannin basu tabbatar da batan babban malamin addinin Kiristan ba, wayoyinsa da ake ta kira basu shiga

Wasu mazauna Enugu sun fita tituna da lungunan jihar inda suke zanga-zanga kan batan dabon da Ejike Mbaka, daraktan Adoration Ministry Enugu Nigeria (AMEN) yayi.

Akwai rahotannin da ke yawo duk da ba a tabbatar da su ba na batan babban malamin addinin Kiristan.

Da farko zai halarci taron addu'o'i da safiyar Laraba, amma ba a gan shi ba.

KU KARANTA: Da duminsa: Majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaro da IGP

Da duminsa: Mabiyan Father Mbaka sun fito zanga-zanga bayan bacewarsa a Enugu
Da duminsa: Mabiyan Father Mbaka sun fito zanga-zanga bayan bacewarsa a Enugu. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yahaya Bello: Buhari na kaunar matasan Najeriya, yana basu dama masu yawa

Mutane da yawa da suka halarci wurin addu'o'in da safe sun hau kan tituna inda suke bukatar sanin inda malamin yake.

An gansu da ganyayyaki tare da rassan bishiyoyi inda suke wake-waken kara a kan manyan titunan jihar.

Har a halin yanzu TheCable bata samu babban malamin ba a wayarsa da ta dinga kira.

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, Shehu Sani, tsohon sanatan Kaduna, yace akwai matukar hatsari abinda gwamnatin take yi na nuna halin ko in kula a kan garkuwa da 'yan jami'ar Greenfield da aka yi.

Sama da dalibai 20 ne aka sace daga jami'a mai zaman kanta yayin da 'yan bindiga suka kutsa makarantar a ranar 18 ga watan Afirilu.

Wadanda suka sace daliban sun bukaci kudi har naira miliyan 800 amma sai suka kashe biyar daga cikin daliban bayan an kasa biya masu bukatarsu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel