Da duminsa: Gwamnatin tarayya ta amince da fara amfani da fasahar 5G
- Daga karshe, gwamnatin tarayya ta bayyana cewa za a fara amfani da fasahar 5G
- Hakan ya biyo bayan yarjejeniyar da aka saka hannu tsakanin NCC da Nigcomsat
- Kamar yadda aka tabbatar, kaddamar da fasahar a kasar nan zata kawo kudin shiga ga FG
Daga bisani, cece-kucen da ke tattare da fasahar 5G ta zo karshe bayan gwamnatin tarayya ta kammala shirin rungumar fasahar.
Wannan ya biyo bayan saka hannu kan wata yarjejeniya tsakanin hukumar sadarwa ta kasa (NCC) a ranar Laraba da kuma hukumar sadarwa ta tauraron dan Adam (Nigcomsat).
Vanguard ta ruwaito cewa, a karkashin yarjejeniyar, NIGOSAT zata zuba 160Megs na C-Band wanda gwamnati za ta samu kudin shiga daga siyar dashi ga kamfanonin sadarwa ta karkashin NCC.
KU KARANTA: Da duminsa: Majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaro da IGP
KU KARANTA: Juyin mulki: Hedkwatar tsaro ta ja kunnen sojoji da 'yan siyasa da kakkausar murya
Yarjejeniyar kamar yadda mataimakin shugaban NCC, Farfesa Umar Danbatta, ta samu sa albarkar National Frequency Management Council, wanda ya samu shugabancin Ministan sadarwa da tattalin arziki mai dogaro da fasahar zamani, Dr Isa Ibrahim Pantami.
A bangaren cece-kucen dake tattare da fasahar 5G, EVC tace tuni ta yi bincike a bangaren tsaro da kuma lafiya kuma hukumar ta bazama wurin wayarwa jama'a kai.
Tun dai a farkon 2020 ne maganar fasahar 5G ta janyo cece-kuce a kasar nan.
A wani labari na daban, Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana kaunar matasa kuma tana son ganinsu a cikin harkar shugabanci.
Gwamnan yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na kauna kuma yana fifita matasa a kasar nan inda ya kara da cewa hakan alama ce dake nuna goyon bayansa ga bukatar baiwa matasa mulki.
A watan Mayun 2018 shugaban kasan yasa hannu a kan kudirin rage shekarun takarar majalisar jiha da majalisar wakilai daga 30 zuwa 25, majalisar dattawa da gwamnoni daga 35 zuwa 30 da kuma kujerar shugaban kasa daga 40 zuwa 35.
A yayin zantawa da shirin gari ya waye na gidan talabijin na Channels a ranar Talata, Bello yace lokaci yayi da matasa zasu karba ragamar mulkin kasar nan.
Asali: Legit.ng