Gumi: Ban san komai a kan N800,000 da aka karba ba domin sako daliban Afaka

Gumi: Ban san komai a kan N800,000 da aka karba ba domin sako daliban Afaka

- Fitaccen Malamin addinin Islama, mazaunin garin Kaduna, ya musanta zarginsa da ake da hada iyayen daliban Afaka da wani mutum

- Ya ce zargin da aka masa na hada su da wani mutum har ya karba musu N800,000 rashin hankali ne kuma bai san komai a kai ba

- Daya daga cikin iyayen daliban Afaka tace Gumi ya hada su da wani Ahmed inda wani bafulatani ya karba N800,000 a wurinta

Ahmad Gumi, fitaccen Malamin addinin Islama, ya musanta sanin komai a kan N800,000 da aka biya domin a sako daliban makarantar Afaka da aka sace a jihar Kaduna.

A watan Maris ne 'yan bindiga suka kai hari kwalejin gandun daji dake Afaka a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna suka sace dalibai 39.

Amma kuma tuni aka sako 10 daga cikin daliban inda guda 29 aka sako su a ranar Laraba, 5 ga watan Mayu.

A ranar Laraban kafin a sako daliban, iyayensu sun yi zanga-zanga a gaban majalsar dattawa domin bukatar a sakar musu 'ya'yansu.

KU KARANTA: Shehu Sani ga El-Rufai: Idan kana da wata hanyar ceto da ba kudin fansa ba, ka nuna mana

Gumi: Ban san komai a kan N800,000 da aka karba ba domin sako daliban Afaka
Gumi: Ban san komai a kan N800,000 da aka karba ba domin sako daliban Afaka. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: Majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaro da IGP

A yayin zantawa da wani gidan talabijin, daya daga cikin iyayen daliban ta zargi Gumi da kaisu wurin wani bafulatani mai suna Ahmed wanda ya karba N800,000 a hannunsu.

"Muna ta zuwa taro, An kaimu gidan Gumi wanda yace mu samu wani Ahmed. Na manta sunanshi," tace.

“An gayyaci wani bafulatani kuma mun hada N800,000 amma yace kudin kaiwa da kawowa ne. Na yi kuka inda nace mishi bani da miji kuma ni kadai nake kula da yarana, amma sai yace hakan bai dame shi ba."

Amma Gumi ya sanar da TheCable cewa wannan zargin "rashin hankali ne" yayin da aka tuntubeshi a ranar Laraba.

Malamin wanda aka san yana iya tunkarar 'yan bindigan, yace bai san da wannan cinikayya ba.

"Wannan rashin hankali ne. Ban san komai a kan wata cinikayya ta kudi ba," yayi martani a sakon kar ta kwana.

A wani labari na daban, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, a ranar Talata ya bada umarnin damke wasu shugabannin kungiyoyi 13 dake yankin Gangare dake Mile 12 a Ketu a kan zarginsu da hannun wurin tada zaune tsaye.

Shugabannin sun jagoranci wasu matasa ne wurin tada tarzoma a kan wani furuci da ake zargin wani Alhaji Alidu Mohammed yayi, wanda ake ikirarin rashin da'a ne da batanci ga Annabi Muhammad.

Bayan shugabannin 13 sun bada umarni, wasu 'yan daba dake yankin a ranar 30 ga watan Afirilun 2021 wurin karfe 3:30 na yammaci sun tada tarzoma, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel