Wata Mummunar Gobara Ta Laƙume Gidaje 100 a Jihar Taraba, Mutum Biyu Sun Rigamu Gidan Gaskiya

Wata Mummunar Gobara Ta Laƙume Gidaje 100 a Jihar Taraba, Mutum Biyu Sun Rigamu Gidan Gaskiya

- Wata gobara ta yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu yayin da ta laƙume gidaje sama da 100 a ƙauyen Bandawa, jihar Taraba

- Rahotanni sun tabbatar da cewa lokacin da wutar ta kama, mafi yawancin yan ƙauyen sun fita zuwa Gonakinsu

- Shugaban ƙauyen yayi kira ga masu ruwa da tsaki a jihar da su taimakawa waɗanda abun ya shafa

Wata gobara da ta ɓarke da sanyin safiya a ƙauyen Bandawa, karamar hukumar Karim-Lamiɗo ta hallaka mutun biyu tare da ƙone gidaje a ƙalla 100.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Har Yanzun Hukumar DSS Bata Damƙe Sheikh Gumi Ba, Tsohon Darakta

Rahoton Dailytrust ya bayyana cewa gobarar ta laƙume sama da rabin gidajen Ƙauyen, kuma har yanzun ba'a gano musabbabin tashinta ba.

Rahotanni daga wata majiya a ƙauyen sun ce gobarar ta jawo hasara ta maƙudan kuɗaɗe, wanda suka haɗa da; kayayyakin abinci, dabbobin kiyo da dai sauran su.

Wata Mummunar Gobara Ta Laƙume Gidaje 100 a Jihar Taraba, Mutum Biyu Sun Rigamu Gidan Gaskiya
Wata Mummunar Gobara Ta Laƙume Gidaje 100 a Jihar Taraba, Mutum Biyu Sun Rigamu Gidan Gaskiya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin mazauna ƙauyen, Mr. Bitrus John, yace lokacin da wutar ta kama mafi yawancin yan ƙauyen basa nan, sun tafi gonakin su domin gudanar da aiki.

Yace hayaƙin da suka gani yana fitowa daga ɓangaren ƙauyen shine ya jawo hankalin manoman suka fahimci akwai wani abu dake faruwa.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Majalisa Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Dakatar da Shirin Ƙidaya 2021

John ya ƙara da cewa kafin mutanen su iso ƙauyen nasu, wutar ta riga ta laƙume gidaje sama da 100.

Yace wasu yan uwa biyu sun rasa rayukansu a cikin ɗaki ta sanadiyyar wutar.

John yace: "Mafi yawancin gidajen suna da rufin kwano wanda hakan yasa wutar ta rinƙa yaɗuwa daga nan gidan zuwa can. Mata da ƙananan yara dake cikin garin ba zasu iya shawo kan wutar ba."

Anashi jawabin, shugaban ƙauyen, Mr Mathias Manyi, ya miƙa roƙonsa ga ƙaramar hukumar Karin-Lamiɗo da kuma gwamnatin jihar Taraba su taimakawa waɗanda mummunar gobarar ta yiwa ɓarna.

Yace da yawa daga cikin waɗanda abun ya shafa sun rasa duk wani abu da suka mallaka harda kayayyakin abincinsu.

A wani labarin kuma Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kareshi

Sanata Rochas Okorocha yace shugaba Buhari yana bashi tausayi saboda shi kadai ne yake ƙoƙarin gyara ƙasar nan.

Okorocha yace gaba ɗaya ministoci, daraktoci da dukkan na kusa da shugaban sun yi gum da bakinsu basa cewa komai wajen kare shugaban.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel