Dalilin da Yasa Har Yanzun Hukumar DSS Bata Damƙe Sheikh Gumi Ba, Tsohon Darakta

Dalilin da Yasa Har Yanzun Hukumar DSS Bata Damƙe Sheikh Gumi Ba, Tsohon Darakta

- Tsohon daraktan hukumar tsaro DSS yace yana da matuƙar wahala hukumar ta iya yanke hukuncin kama malamin addinin musulunci, Ahmad Gumi.

- Tsohon daraktan ya bayyana dalilinsa da cewa idan ka kama shi a yanzun to zaka tsokalo masu goyon bayansa ne ko kuma waɗanda yake wa aiki

- A cewarsa idan kuma baka kama shi ba mutane zasu ce har yanzun bai shiga hannu ba bayan kuma masu aikata aiki irin nasa an kama su

Tsohon daraktan hukumar tsaro DSS, Mike Ejiofor, yace hukumar ta shiga cikin kokwanto ne akan ko ta kamo shahararren malamin addinin islama, Ahmad Gumi, ko kuma ta kyaleshi, kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Majalisa Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Dakatar da Shirin Ƙidaya 2021

Tsohon darktan yace ba dai-dai bane shahararren malamin ya fito fili ya buƙaci babban bankin Najeriya CBN ya biya 100 miliyan kuɗin fansa, wanda yan bindigar da suka sace ɗaliban jami'ar Greenfield suka buƙata.

Dalilin da Yasa Har Yanzun Hukumar DSS Bata Damƙe Sheikh Gumi Ba, Tsohon Darakta
Dalilin da Yasa Har Yanzun Hukumar DSS Bata Damƙe Sheikh Gumi Ba, Tsohon Darakta Hoto: Vanguardngr.com
Asali: UGC

A jawabin da tsohon daraktan yayi kan dalilin rashin kama malamin yace:

"Idan ka kamashi to ka tsokano mutanen dake goyon bayansa ko kuma mutanen da yake yiwa aiki. Idan kuma baka kama shi ba mutane zasu ce har yanzun an gaza kamashi bayan kuma masu aiki irin nasa an riga da an damƙe su."

"Saboda haka wannan wani yanayi ne mai hatsari da yake buƙatar a rike lamarin da kulawa."

KARANTA ANAN: Gwamnoni Sun Gana da Sufetan Yan Sanda Na Ƙasa, Sun Tattauna Muhimman Abubuwa a Kan Tsaro

A ranar Talata data gabata Gumi ya buƙaci CBN ya biya 100 miliyan kuɗin fansar ɗaliban jami'ar Greenfield da aka sace tun kafin lokaci ya ƙure.

Aƙalla ɗalibai da ma'aikata 23 ne yan bindiga suka yi awon gaba dasu daga jami'ar Greenfield Kaduna ranar 20 ga watan Afrilun wannan shekarar da muke ciki.

Sai dai bayan kwanaki kaɗan yan bindigan suka kashe biyar daga cikin ɗaliban da suka sace daga jami'ar sannan suka bukaci a biya 100 miliyan kuɗin fansar ragowar ko kuma su kashe su.

A wani labarin kuma Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kareshi

Sanata Rochas Okorocha yace shugaba Buhari yana bashi tausayi saboda shi kadai ne yake ƙoƙarin gyara ƙasar nan.

Okorocha yace gaba ɗaya ministoci, daraktoci da dukkan na kusa da shugaban sun yi gum da bakinsu basa cewa komai wajen kare shugaban.

Asali: Legit.ng

Online view pixel