Gwamna Abubakar Sani Bello Ya Kori Kwamishinan Ayyuka a Jiharsa

Gwamna Abubakar Sani Bello Ya Kori Kwamishinan Ayyuka a Jiharsa

- Alhaji Abubakar Sani Bello ya sallami kwamishinan ayyuka da gine-gine da cigaba, Injiniya Ibrahim Muhammad Panti daga aiki

- Mrs Mary Noel-Berje, babban sakataren watsa labarai na gwamnan ne ta bada sanarwar duk da cewa ba a fada dalilin sallamarsa ba

- Sanarwar ta ce za a maye gurbin Ibrahim Muhammad Panti da Alhaji Mamman Musa tsohon kwamishinan ma'aikatar tsare-tsare

Gwamnan jihar Niger, Alhaji Abubakar Sani Bello ya sallami kwamishinan ayyuka da gine-gine da cigaba na jiharsa, Injiniya Ibrahim Muhammad Panti daga aiki, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Babban sakataren watsa labarai na gwamnan, Mrs Mary Noel-Berje ce ta bayyana hakan cikin wani sanarwa da ta fitar a ranar Alhamis 6 ga watan Mayun shekarar 2021.

Gwamna Abubakar Sani Bello Ya Kori Kwamishinan Ayyuka a Jiharsa
Gwamna Abubakar Sani Bello Ya Kori Kwamishinan Ayyuka a Jiharsa. Hoto: @thecableng
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Jonathan Ya Yi Jinjina Ga Tsohon Mai Gidansa Ƴar’Adua Shekaru 11 Bayan Rasuwarsa

Nole-Berje ba ta bada dalilin da yasa aka kori kwamishinan daga aiki ba, wanda kuma shine shugaban kwamitin albashi na jihar.

Noel-Berje ta ce Kwamishinan Tsare-Tsare, Alhaji Mamman Musa shine zai kama aiki a matsayin kwamishinan ayyuka da gine-gine na jihar yayin da kwamishinan Kudi, Alhaji Zakari Abubakar zai rika kula da ma'aikatar tsare-tsare tare da ma'aikatar kudi.

KU KARANTA: Gumi Ya Faɗa Mana Gaskiya, Yana Tare Da Ƴan Ta’adda Ne Ko Ƴan Nigeria, Adamu Garba

"Mamman Musa zai mika mulkin Ma'aikatar tsare-tsare ga Zakari, yayin da Injiniya Ibrahim Mohammed Panti zai mika mulki ga Mamman Musa nan take," a cewar sanarwar.

A wani labarin daban tsohon mataimakin shugaban kasa Mr Atiku Abubakar, a ranar Litinin, ya zargi gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da musgunawa kafafen watsa labarai da yi wa yan kasa barazana idan sun bayyana ra'ayoyinsu.

Atiku ya yi wannan zargin ne cikin wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter @atiku domin bikin ranar Yan Jarida na Duniya.

Ya bayyana cewa idan ana tauye hakkin mutane a mulkin demokradiyya, hakan zai kawo rashin jituwa tsakanin mutane da gwamnatin kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: