Gobarar Kasuwar Katsina: Kwamiti Ya Mika Rahoto, an Bayyana Yawan Kadarorin da Aka Rasa

Gobarar Kasuwar Katsina: Kwamiti Ya Mika Rahoto, an Bayyana Yawan Kadarorin da Aka Rasa

- Kwamitin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa domin ya gudanar da bincike a kan musabbabin gobarar data faru a babbar kasuwar jihar kwanakin baya ya miƙa rahotonsa

- A rahoton, kwamitin yace ya gano cewa gobarar ta laƙume kyayyaki da suka kai na 902 miliyan, sannan kuma rashin kyaun wutar lantarki ne musabbabin tashin wutar

- Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa ma'aikata da kuma masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar, sune zasu taimaka a tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa

Kwamitin da gwamnatin jihar Katsina ta kafa domin ya binciko musabbabin gobarar data faru a babbar Kasuwar Katsina ya miƙa rahotonsa, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Kungiyar Ƙwadugo Ta Gargaɗi Gwamnatin Tarayya Karta Kuskura Ta Zabtarewa Ma’aikata Albashi

Shugaban kwamitin, Alhaji Tasi'u Dandagaro, yayin da yake miƙa rahoton ga gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari a gidan gwamnati ranar Laraba, yace rashin tsarin haɗakar wayoyin wutar lantarki shine musabbabin gobarar.

Ya kuma ƙara da cewa gobarar ta laƙume kadarori da suka kai na kimanin miliyan N902m.

Gobarar Kasuwar Katsina: Kwamiti Ya Mika Rahoto, an Bayyana Yawan Kadarorin da Aka Rasa
Gobarar Kasuwar Katsina: Kwamiti Ya Mika Rahoto, an Bayyana Yawan Kadarorin da Aka Rasa Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Ɗandagaro yace yan kasuwa 685 ne gobarar ta shafe su kai tsaye, yayin da gobarar ta laƙume shaguna 605.

Sannan kuma yace akwai wasu yan kasuwa 56 dake jikin kasuwar suma gobarar ta shafe su, sai kuma wasu yan kasuwa 21 da aka sace wa kayayyakin su lokacin gobarar.

Shugaban ƙwamitin yace:

"A kiyasin da mukayi, idan aka haɗa dukkan abubuwan da suka salwanta, gobarar ta laƙume kadarorin da suka kai darajar kuɗi N902,138,500, amma wannan rahoton bai ƙunshi tsarin ginin da ya salwanta ba."

"Kwamitin mu ya gano cewa rashin tsarin da yakamata na wayoyin wutar lantarki tare da haɗa su da kayayyakin siyarwa shine musabbabin tashin wutar."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sace Mutum 100 a Jihar Neja

A jawabinsa, gwamna Aminu Bello Masari, yace ma'aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa zasu bada gudummuwa wajen tallafa wa waɗanda lamarin ya shafa.

Masari yace: "Ma'aikatan gwamnati da masu riƙe da muƙaman siyasa su ke cinye kashi 80% na kuɗaɗen shigar gwamnatin jihar, Saboda haka akwai buƙatar su taimaka wajen tallafa wa waɗanda gobarar ta shafa."

Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatin jihar zata ƙaddamar da wani kwamiti, waɗanda zasu binciko mana hanyar da za'a bi a warware rahoton da wannan kwamitin ya gabatar.

A wani labarin kuma Wata Mummunar Gobara Ta Laƙume Gidaje 100 a Jihar Taraba, Mutum Biyu Sun Rigamu Gidan Gaskiya

Wata gobara ta yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu yayin da ta laƙume gidaje sama da 100 a ƙauyen Bandawa, jihar Taraba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa lokacin da wutar ta kama, mafi yawancin yan ƙauyen sun fita zuwa Gonakinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262