Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sace Mutum 100 a Jihar Neja

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sace Mutum 100 a Jihar Neja

- Wasu yan bindiga sun kai hari garin Shadaɗi dake ƙaramar hukumar Mariga a jihar Neja, inda suka hallaka mutum 8 tare da jikkata wasu huɗu

- Mazauna garin sun tabbatar da kai harin tare da cewa yan bindigan sun yi awon gaba da mutane sama da 100

- Gwamnatin jihar ta Neja ta tabbatar da kai harin amma ta musanta adadin da wasu ke yaɗawa cewa maharan sun sace mutane sama da 100

Yayin da matsalar tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a wasu jihohin Najeriya, jihar Neja na cikin waɗanda abun yake ta ƙara tsananta.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Har Yanzun Hukumar DSS Bata Damƙe Sheikh Gumi Ba, Tsohon Darakta

Mazauna wasu ƙauyuka a jihar Neja sun bayyana cewa yan bindiga sun kai musu wani mummunan hari, tare da yin awon gaba da mutane sama da 100 a garin Shadaɗi.

Ɗaruruwan mutanen garin Shadaɗi dake ƙaramar hukumar Mariga sun ƙauracewa gidajen su tun bayan harin da yan bindigan suka kai garin su.

Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sace Mutum 100 a Jihar Neja
Da Ɗumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Sace Mutum 100 a Jihar Neja Hoto: channelsrv.com
Asali: UGC

Ɗaya daga cikin mazauna garin ya shaidawa BBC cewa gungun yan bindiga da zasu iya kaiwa 1000 ne suka kai hari garin kuma suka kashe mutane takwas tare da jikkata wasu mutum huɗu.

Mutumin wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa yace mafi yawancin yan garin sun gudu zuwa wasu ƙauyuka dake maƙwabtaka da su domin tseratar da rayuwar su.

KARANTA ANAN: Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kareshi

Anashi ɓangaren, kwamishinan yaɗa labarai na jihar Neja, Alhaji Sani Idris, ya tabbatar da faruwar lamarin amma ya musanta adadin waɗanda ake yaɗawa cewa yan bindigar sun sace.

Kwamishinan yace: "Adadin mutanen da yan bindigan suka sace bai kai 100 ba, yanzun haka muna kan gudanar da bincike domin gano mutum nawa ne harin ya ritsa da su."

Kwamishinan ya ƙara da cewa tuni gwamnatin jihar Neja ta nemi taimakon gwamnatin tarayya domin magance faruwar lamarin nan gaba.

A wani labarin kuma Buhari Yayi Allah Wadai da Sabon Harin da Wasu Yan Bindiga Suka Kai Benuwai, Ya Faɗi Matakin da Zai Ɗauka

Shugaba Buhari ya nuna matuƙar rashin jin daɗinsa bisa wasu jerin hare-hare da yan bindiga suka kai jihohin Benuwai da Anambra.

Buhari yayi wannan jawabi ne a cikin wani saƙo da babban mai bashi shawara ta musamman kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, ya fitar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel