Abin da mutane ke fada game da Shugaba ‘Yar’adua yau a Twitter shekaru 11 da rasuwarsa

Abin da mutane ke fada game da Shugaba ‘Yar’adua yau a Twitter shekaru 11 da rasuwarsa

A rana irin ta yau ne Ummaru Musa ‘Yaradua ya rasu ya na kusan shekara 60. Marigayin ya na cikin shugabannin kasan da su ka mutu a kan kujerar mulki.

Ummaru Musa ‘Yaradua ya yi shekaru kusan uku a kan mulki ne sai Ubangiji ya dauki rayuwarsa. Shugaban Najeriyar ya yi ta fama da rashin lafiya.

Legit.ng Hausa ta tattaro maku abin da mutane su ke fada a Twitter a kan wannan Bawan Allah:

“Marigayi shugaba Yaradua ya samu litar fetur a N75, ya dawo da shi N65. Ya shawo kan tattalin arzikin kasa, ya tsaida darajar Dala a kan N145. Lallai abokin talakawa ne. Allah ya jikan rai.” Inji Bolanle Cole.

KU KARANTA: Abubuwa 6 game da rayuwar 'Yar'adua

Halima Gumel ta rubuta: “Ayi amfani da ‘yar damar da ake da ita a wannan Ramadan, ayi wa Marigayi shugaba Ummaru Musa ‘Yaradua addu’a. Ya kasance shugaba na gari.”

“Ba a taba yin shugaban da ya fi Ummaru Musa ‘Yaradua a Najeriya ba. Allah ya jikansa da rahama.”– Dahiru Yasir

Wani Habib Abdulwahab cewa ya yi: “Yau shekara 11 kenan da mu ka rasa gwarzonmu, Malam Ummaru Musa ‘Yaradua, shugaban kasa tsakanin 2007 da 2010. Allah ya sa ya huta a Aljannatul firdausi.”

"Marigayi Umaru Musa Yaradua shi ne rashi mafi girma da Najeriya ta yi tun da aka dawo farar hula. Yau shekara 11 kenan da ya rasu. Shugaba mai shiri da hangen nesa ga Najeriya.” AG Dauda ya yi masa addu’a.

Rayyan A. Tilde ya rubuta: “A wuri na, ‘Yaradua ne shugaban karshe da mu ka yi. Shekara 11 kenan da rasa ka, abubuwa sun sukurkuce mana ta ko ina.”

KU KARANTA: Felacia Adebola ta cika

Abin da mutane ke fada game da Shugaba ‘Yar’adua yau a Twitter shekaru 11 da rasuwarsa
Tsohon Shugaban kasa Ummaru ‘Yar’adua Hoto: www.guardian.ng/politics

Wani mutum yake cewa: “Da Ummaru Musa ‘Yaradua ya yi tsawon rai, da ba ayi shugaban kasar da ya fi shi ba. Amma Ubangiji ya san dalilin dauke mana shi. Allah ya jikansa.”

Reina Fulani Teacher ta ce mutuwar Yaradua ya gigita, ta yi masa addu’ar samun rahama.

A yau da safe ne tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya tuna da maigidansa, Shugaba Umaru Yar'adua a yayin da yake cika shekaru 11 da rasuwa.

Da yake magana a shafinsa na Twitter dazu, Goodluck Jonathan ya ce fatan tsohon shugaba Yar'adua shine samar da zaman lafiya da haɗa kan ƴan kasa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel