Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Majalisa Sun Buƙaci Gwamnatin Tarayya ta Dakatar da Shirin Ƙidaya 2021
- Majalisar wakilai ta ƙasar nan ta buƙaci gwamnatin tarayya ta ɗage shirinta na gudanar da kidayar yawan jama'a da gidaje data shirya yi a wannan shekarar
- Majalisar ta yanke wannan hukuncin ne bayan amincewa da wani kudirin ƙasa da ɗaya daga cikin mambobinta daga jihar Neja ya gabatar mata a zaman yau Laraba.
- Ɗan majalisar dai yace akwai dalilai da dama da idan aka kalle su za'a dakatar da shirin ƙidayar sabida zasu shafi ingancin sakamakon da za'a samu bayan an kammala
Yan majalisar wakilai sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ɗage kidayar jama'a da gidaje data shirya yi a shekarar 2021, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Sanatan APC Ya Caccaki Mutanen Dake Kewaye da Buhari, Yace Babu Mai Iya Ɗaga Murya Don Kareshi
Wannan kiran yazo ne bayan zauren majalisar ya karɓi kudirin ƙasa wanda ɗan majalisa mai wakiltar mazaɓar Bosso/Paikoro a majalisar wakilai ta ƙasa daga jihar Neja, Shehu Beji, ya gabatar mata a zaman ta na yau Laraba.
Yayin da yake gabatar da kudirin, ɗan majalisar yace, akwai dalilai da dama da zasu sa a dakatar da shirin kidayar waɗanda zasu shafi sakamakon da za'a samu bayan an kammala.
Ya ƙara da cewa samun nasarar wannan aikin na ƙidaya zai samu tasgaro sosai saboda matsalar tsaron da yan Najeriya ke ciki a sassa daban-daban na ƙasar nan.
KARANTA ANAN: Ya Kamata CBN Ya Biya 100 Miliyan Na Fansar Ɗaliban Greenfield Tun Kafin Lokaci Ya Ƙure, Sheikh Gumi
"Kodai wasu an tilasta musu barin matsugunin su ko kuma an kassara musu rayuwarsu ta yau da kullum." inji shi.
Sannan kuma Baji ya bayyana cewa babu tabbas ɗin masu ƙidayar zasu samu ingantaccen tsaro a mafi yawancin sassan ƙasar nan da matsalar tsaro ta shafa.
A wani labarin kuma El-Rufa’i Ya Bayyana Yadda Alaƙarsa Tayi Tsami da Jonathan a Mulkinsa, Yace Ya Kusa Tura Shi Gidan Gyaran Hali
Gwamnan Kaduna , Nasir Elrufa'i, ya bayyana yadda alaƙarsa ta yi tsami tsakaninsa da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan.
Yace duk da cewa Jonathan babban amininsa ne tun yana mataimakin gwamnan Bayelsa, amma saida ya matsa masa lamba sabida wasu yan karaɗi sun ziga shi kuma ya ɗauka.
Asali: Legit.ng