Da duminsa: Majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaro da IGP

Da duminsa: Majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaro da IGP

- Majalisar dattawan Najeriya ta sauya ranar ganawa da shugabannin tsaron kasar nan zuwa Alhamis

- Hakan ya biyo bayan taron majalisar tsaro da suka fara a makon jiya kuma suka cigaba a yau Talata a fadar shugaban kasa

- Idan zamu tuna majalisar dattawan ta gayyaci shugabannin tsaron kasar nan a kan tabarbarewar da tsaron kasar yayi

A ranar Talata ne majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaron kasar nan, darakta janar na hukumar binciken sirri da kuma sifeta janar na 'yan sandan Najeriya zuwa ranar Alhamis.

Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya bayyana hakan yayin zaman majalisar.

Lawan yace hafsoshin tsaron da ya kamata su yi wa majalisar dattawa bayani suna taron tsaro na kasa wanda zai kaisu har ranar Laraba.

Ya ce: "Jawabin da muke son ji yana da matukar amfani kuma zai zamo tamkar jagora garemu. Mun mayar da shi zuwa ranar Alhamis."

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Fusatattun matasa sun lallasa kwamandan 'yan sintiri, sun kone motarsa

Da duminsa: Majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaro da IGP
Da duminsa: Majalisar dattawa ta sauya ranar ganawa da hafsoshin tsaro da IGP. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ganduje ya karawa malaman makaranta shekarun ritaya, daga 60 zuwa 65

A ranar Talatan makon da ya gabata ne majalisar dattawan bayan tattaunawa ta yanke hukuncin gayyatar shugabannin tsaron kasan a kan yadda lamarin tsaro ke cigaba da tabarbarewa a kasar nan.

Ta kara da yanke cewa zata samu ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari domin samo hanyar magance matsalar tsaron da ta addabi kasar nan.

Lawan ya ce: "Idan zaku tuna, a ranar Laraba ne muka sanar da cewa, shugaban ma'aikatan tsaro, hafsoshin tsaro da kuma sifeta janar na 'yan sanda tare da darakta janar na NIA zasu zo a yau da karfe 11 na safe domin bayani kan halin da kasar nan ke ciki.

"A yau majalisar tsaron kasa na cigaba da taron da ta fara a makon da ya gabata. Don haka shugabannin tsaron da aka gayyata ba zasu iya zuwa ba.

"Ba mu da tabbacin ko zasu kammala taron a yau. Mun sauya lokacin da zasu zo zuwa ranar Alhamis, 6 ga watan Mayu."

A wani labari na daban, farar hula shida tare da jami'in tsaro daya ne suka rasa rayukansu yayin da mayakan Boko Haram suka kai farmaki garin Ajari dake karamar hukumar Mafa ta jihar Borno a ranar Litinin.

Karamar hukumar Mafa ce inda Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya fito. Kamar yadda sakataren karamar hukumar, Mohammed Sherrif, yace, "'Yan ta'addan sun tsinkayi garin wurin karfe 1 na dare kuma suka dinga bankawa gidajen jama'a wuta sannan suka kashe farar hula shida da wani jami'in tsaro daya."

Mafa tana da nisan kusan kilomita 30 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, jaridar The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng