Batanci ga Annabi: Rundunar 'yan sandan Legas ta bada umarnin cafke mutum 13

Batanci ga Annabi: Rundunar 'yan sandan Legas ta bada umarnin cafke mutum 13

- Hakeem Odumosu, kwamishinan 'yan sandan jihar Legas ya bada umarnin damke wasu mutum 13

- An gano cewa su suka bada umarnin tada zaune tsaye a yankin Gangare bayan an zargi wani da batanci ga Annabi

- Matasan da shugabannin kungiyoyin 13 suka ba umarni sun kone motoci 2, sun kashe mutum 1 tare da kona gida 1

Kwamishinan 'yan sandan jihar Legas, Hakeem Odumosu, a ranar Talata ya bada umarnin damke wasu shugabannin kungiyoyi 13 dake yankin Gangare dake Mile 12 a Ketu a kan zarginsu da hannun wurin tada zaune tsaye.

Shugabannin sun jagoranci wasu matasa ne wurin tada tarzoma a kan wani furuci da ake zargin wani Alhaji Alidu Mohammed yayi, wanda ake ikirarin rashin da'a ne da batanci ga Annabi Muhammad.

Bayan shugabannin 13 sun bada umarni, wasu 'yan daba dake yankin a ranar 30 ga watan Afirilun 2021 wurin karfe 3:30 na yammaci sun tada tarzoma, Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Bidiyon fasto tana yi wa 'yan cocinta tofin Allah tsine a kan sun ki tara mata kudin bikin bazday

Batanci ga Annabi: Rundunar 'yan sandan Legas ta bada umarnin cafke mutum 13
Batanci ga Annabi: Rundunar 'yan sandan Legas ta bada umarnin cafke mutum 13. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Yan Boko Haram sun kutsa garinsu Zulum, sun sheƙe rayuka 7, sun kone gidaje

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Legas, Muyiwa Adejobi, a wata takarda da ya fitar, yace umarnin kamen ya biyo bayan tattaunawa ne da aka yi tsakanin wasu daga cikin shugabannin da kwamishinan 'yan sandan jihar a hedkwatarsu dake Ikeja a ranar Talata.

Adejobi ya ce sakamakon binciken farko, an gano cewa ana zargi kwamandan 'yan sintirin Gangare, Alhaji Alidu Mohammed da rashin da'a da kuma batanci ga Annabi kuma 'yan daban sun kai masa farmaki.

Ya ce 'yan daban sun bankawa motoci biyu wuta, sun farfasa gidansa kafin su sanyawa wani gidan Alhaji Mamuda wuta.

"A martanin wannan tashin hankalin, kwamishinan 'yan sandan ya tura jami'ai inda suka kama mutum 45.

“A sakamakon wannan hargitsin, Papa Mohammed, wanda aka sokawa wuka a ranar ya rasu bayan an kai shi asibiti.

“A kokarin dawo da zaman lafiya da doka a yankin, kwamishinan 'yan sanda a ranar Talata ya bada umarnin damke shugabannin kungiyoyin dake yankin," yace.

A wani labari na daban, hedkwatar tsaron Najeriya ta ja kunnen 'yan siyasa da manyan dakarun sojin kasar nan a kan shirya juyin mulki.

A wata takarda da hedkwatar tsaron ta fitar a ranar Litinin ta hannun Onyema Nwachukwu, mai magana da yawunta, yace hankalinsu ya kai kan wani tsokacin da Robert Clarke, babban lauya yayi na cewa a mika mulkin kasa ga soji.

Rundunar sojin ta tsame kanta daga wannan tsokacin kuma ta kwatanta shi da mai zagon kasa da damokaradiyya tare da cewa tana biyayya ga mulkin kasar nan, The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng