Da Dumi-Dumi: Ba Mu Muka Kwamushe Fasto Mbaka Ba, inji DSS

Da Dumi-Dumi: Ba Mu Muka Kwamushe Fasto Mbaka Ba, inji DSS

- Hukumar tsaro ta farin ta karyata zargin ta da ake da kwamushe Fasto Mbaka biyo bayan maganganunsa

- DSS ta bayyanawa jaridar Punch karara cewa, ba ita ta kame Faston ba, kuma ba ta da masaniya

- A jihar Enugu, an gudanar da zanga-zangar nuna damuwar batan Fasto Mbaka a wannan makon

Hukumar Tsaro ta Farin Kaya ta ce ba ita ta ke tsare da malamin addinin Kirista Rev. Fr. Ejike Mbaka ba.

Kakakin hukumar DSS, Peter Afunnaya ne ya bayyana haka a wani sakon tes da aka aika wa jaridar The PUNCH a ranar Laraba.

“Mbaka ba ya tare da DSS, don Allah,” Afunnaya ya rubuta a martaninsa ga wakilin Punch a tambayar da ya yi masa.

KU KARANTA: Felicia Adebola, Marubuciyar da Ta Rubuta Taken Alkawarin Najeriya ta Mutu

Da Dumisa: Ba Mu Muka Kwamushe Fasto Mbaka Ba, inji DSS
Da Dumisa: Ba Mu Muka Kwamushe Fasto Mbaka Ba, inji DSS Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rikici ya barke a binciken inda malamin addinin yake a ranar Laraba tare da rahoton zanga-zanga a jihar Enugu kan Mbaka da ake zargin wani jami’in tsaro da har yanzu ba a gano shi ba ya tafi dashi.

Lokacin da aka tuntubi jami'an Diocese na jihar Enugu, wanda Fr. Mbaka ke ciki, wasu daga cikinsu sun ce bai bata ba yayin da wasu suka ce ba za su iya tabbatar da inda yake ba.

KU KARANTA: An Kame Tsohuwa Mai Shekaru 80 Da Jikarta Da Laifin Sayar Da Hodar Iblis

A wani labarin, An yi zaman murna a jihar Enugu ranar Laraba bayan da Daraktan ruhaniya na Adoration Ministry dake Enugu, Ejike Mbaka, ya sake bayyana bayan damuwar rashin sanin inda yake ya haifar da rudani a jihar.

Lokacin da Mbaka ya dawo a cikin mota ‘yan mintoci kadan bayan karfe 2 na yamma, an ga magoya bayansa suna ihu 'Father Mbaka, Oh! barka da dawowa gida !."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.