Bill Gates, Jeff Bezos da Sauran Manyan Attajirai 3 da Suka Saki Matansu a Tarihi da Arzikinsu

Bill Gates, Jeff Bezos da Sauran Manyan Attajirai 3 da Suka Saki Matansu a Tarihi da Arzikinsu

Soyayyar shekaru da dama ta zo karshe a wata sanarwa da ta zo wa mabiya shafukan soshiyal midiya a bazata kuma har yanzu ana kan tattauna batun – Bill da Melinda Gates sun rabu.

Amma, a zahiri ba su ne ma'auratan attajirai da aurensu ya mutu ba kuma tabbas ba zai zama na ƙarshe ba. Legit.ng ta zakulo 5 daga cikin saki mafi tsada a tarihi.

Bill Gates, Jeff Bezos da Sauran Manyan Attajirai 3 da Suka Saki Matansu a Tarihi da Arzikinsu
Bill Gates, Jeff Bezos da Sauran Manyan Attajirai 3 da Suka Saki Matansu a Tarihi da Arzikinsu Hoto: Picture alliance, David Swanson
Asali: Getty Images

1. Jeff Bezos da Mackenzie Bezos (dala biliyan 35)

Mutuwar auren Jeff Bezos da Mackenzie Bezos a ranar 5 ga Yulin, 2019 ba wai ya kasance saki mafi tsada ba ne kawai illa ya wargaza rukunin jerin attajirai mata, a cewar GQIndia.

Wannan ya kasance ne saboda Mackenzie ta zama mace ta uku mafi arziki a duniya biyo bayan sasantawar rabuwar auren da ya kai ta ga samun kaso 4% na hannun jarin Amazon wanda ya haura dala biliyan 35.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Tsaro a Fadar Shugaban Kasa

2. Alec Wildenstein da Jocelyn Wildenstein (dala biliyan 3.8)

Attajiri Alec Wildenstein ya rabu da mai dakinsa Jocelyn Wildenstein a 1999.

Kafin duniya ta san da batun rabuwar auren Bezos, ma’auratan wadanda suka shafe tsawon shekaru 21 suna tare sune na daya a wannan rukunin.

Rabuwarsu ta sa matar za ta riƙa samun maƙudan kuɗi har dala miliyan 100 kowace shekara har tsawon shekara 13 ƙididdigar kuɗin da ta kai dala biliyan 3.8.

3. Bill da Sue Gross (dala biliyan 1.3)

Daya daga cikin mutuwar aure mafi muni a tarihi, ita ce rabuwar Bill da Sue a shekarar 2016. Lamarin ya kai mutum daya kasa sannan kuma ya daukaka dayan, Forbes ta ruwaito.

Hakan ya kasance ne yayinda Sue ta samu dala biliyan 1.3 har da mallakar gida a Laguna da aka ƙiyasta kuɗinsa kan dala miliyan 36 da kuma wani zane da ta siyar kan dala miliyan 35. Nan take ta zama biloniya.

A nashi bangaren, Bill bai farfado daga rikicin rabuwar auren ba ta fuskacin arziki domin dukiyarsa ta ragu.

KU KARANTA KUMA: Father Mbaka Ya Yi Sabon Hasashe, Ya Bayyana Abinda Zai Faru Ga Gwamnatin Buhari Idan Aka Kai Masa Hari

4. Harold Hamm da Sue Ann Arnall (dala miliyan 975)

Harold Hamm da Sue Ann Arnall sun kawo karshen auren su na tsawon shekaru 26 inda Harold ya rubutawa Sue takardar kudi na dala miliyan 975 tunda ba su da matsala.

Ta amince da sulhun inda kawai sai ta daukaka kara daga baya a kokarinta na mallakar wani bangare na kashi 75% na Kasuwancin Harold wanda ya kai dala biliyan 13.7. Amma ba ta yi nasara ba.

5. Bill and Melinda Gates

Ma'auratan da suka samar da gidauniya mafi karfin arziki a duniya, Bill da Melinda Gates sune na baya-baya a jerin bayan sanarwar hadin gwiwa da suka wallafa a shafin su na Twitter a ranar Litinin, 3 ga Mayu, 2021.

Kodayake ba a bayyana cikakken bayani game da mutuwar aurensu ba, tabbas zai kasance ɗaya daga cikin mutuwar aure mafi tsada idan aka yi la’akari da Bill Gates yana da dala biliyan 129.9.

A baya mun kawo cewa Bill Gates, attajirin duniya kuma wanda ya kafa kamfanin kwamfuta na Microsoft ya sanar da shirinsa na rabuwa da mai dakinsa Belinda.

Bill da Melinda sun sanar da labarin ne a shafukansu na Twitter a ranar Litinin inda suka ce sun dauki wannan matakin ne bayan nazari sosai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel