Yanzu Yanzu: Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Tsaro a Fadar Shugaban Kasa

Yanzu Yanzu: Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Tsaro a Fadar Shugaban Kasa

- Shugaba Muhammadu Buhari yana jagorantar taron majalisar tsaro a fadar Villa da ke Abuja

- Taron ci gaban wanda aka dage ne a ranar Juma'a da ta gabata

- Mataimakin shugaban kasa, manyan ma'aikatan fadar shugaban kasa da shugabannin tsaro duk sun hallara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na jagorantar ci gaban taron majalisar tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Taron wanda Buhari ya kira a ranar Juma’ar da ta gabata, an dage shi ne zuwa ranar Talata, 4 ga watan Mayu.

KU KARANTA KUMA: Father Mbaka Ya Yi Sabon Hasashe, Ya Bayyana Abinda Zai Faru Ga Gwamnatin Buhari Idan Aka Kai Masa Hari

Yanzu Yanzu: Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Tsaro a Fadar Shugaban Kasa
Yanzu Yanzu: Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Tsaro a Fadar Shugaban Kasa Hoto: @Buharisallau1
Asali: Twitter

Wadanda suka halarci taron sune Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikata na Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (Mai ritaya) da mai ba Shugaban kasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (Mai Ritaya.)

Shugaban ma'aikatan tsaro, Janar Lucky Irabor, shugaban hafsan sojoji; Laftana-Janar Ibrahim Attahiru, Babban hafsan sojojin ruwa; Vice Admiral Awwal Zubairu, da Babban hafsan sojojin sama, Air Marshal Isiaka Amoo duk suna halartar muhimmin taron.

Mukaddashin Sufeto Janar na 'yan sanda, IGP, Usman Baba shi ma ya halarci taron.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Isa Pantami Ya Tsawaita Wa’adin Hade NIN-SIM Har Zuwa 30 Ga Watan Yuni

Hadimin Shugaban kasa, Buhari Sallau ya tabbatar da zaman a wani wallafa da yayi a shafinsa na Twitter.

A gefe guda, hedkwatar tsaro (DHQ) ta gargadi Sojoji da yan siyasa kan suyi hattara da kowani irin shirin yiwa gwamnatin shugaba Buhari juyin mulki.

Kakakin hedkwatar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya yi wannan gargadi ne a jawabin da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 3 ga Mayu, PRNigeria ta ruwaito.

Nwachukwu ya ce hukumar Soji ta samu labarin cewa wani ya bada shawaran mika mulki ga Sojoji domin yiwa kasa garambawul.

Asali: Legit.ng

Online view pixel