Ban Taba Cewa Gwamnati Na Buga Kudi Ba Tun 2015, Amaechi

Ban Taba Cewa Gwamnati Na Buga Kudi Ba Tun 2015, Amaechi

- Ministan Sufurin ƙasar nan, Rotimi Amaechi, ya karyata rahoton da wasu ke yaɗawa akansa a kafafen sada zumunta.

- Rahoton dai ya bayyana cewa ministan ya fallasa wani asiri inda yace sabbin kuɗi gwamnatin tarayya take bugawa tun bayan hawan ta mulki a shekarar 2015

- Sai-dai ministan ya kira wannan rahoton da 'Ƙarya' inda yace shi bashi da ta cewa a ɓangaren ƙera sabbin kuɗi, kuma bai taɓa riƙe wata ma'aikatar kuɗi ba Saboda haka bai san ya lamarin buga kudi yake ba

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana rahoton da ake yaɗawa a kansa cewa sabbin kuɗi gwamnatin tarayya ke bugawa tana amfani dasu tun shekarar 2015 da 'Ƙarya'.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Aka Samu Tsaiko a Dawo da Miliyan £4.2M da Ibori Ya Sace, Malami Yayi Bayani

Ministan ya kuma roƙi yan Najeriya da suyi watsi da duk wani labari da aka buga a kafafen sada zumunta game da lamarin, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Rahoton wanda ya mamaye kafafen sada zumunta ya bayyana cewa ministan ya faɗi haka ne a wata tattaunawa da yayi da manema labarai kafin zaɓen 2019.

Karya ake mun, ni bance Sabbin kuɗi gwamnati ke ƙeraw ba tun 2015, inji Minista
Karya ake mun, ni bance Sabbin kuɗi gwamnati ke ƙerawa ba tun 2015, inji Minista Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Rahoton ya ƙara da cewa, Amaechi yace sai da ko wanne ɗan majalisar zartarwar gwamnati ya rantse ba zai bayyana wa yan Najeriya wannan sirrin na buga sabbin kuɗi ba.

KARANTA ANAN: Gwamnatin Kogi Tayi Cikakken Bayani Kan Kisan da Yan Bindiga Suka Yiwa Kwamishinanta

Yayin da yake maida martani kan rahoton a wani jawabi da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labari, Taiye Elebiyo-Edeni, ya fitar, yace shi baima cancanta yayi magana akan irin waɗannan lamurran ba na buga sabbin kuɗi

Yace: "Bantaɓa rike wata ma'aikatar kuɗi ba, saboda haka ni ban cancanta a matsayin da nike inyi magana a kan ƙera sabbin kuɗi ga tattalin arziƙin ƙasa ba."

"Ina baiwa yan Najeriya shawara musamman masu son samun bayanai a kan ƙera sabbin kuɗi da su nemi hukumar data dace da buƙatarsu, ba wai suzo suna yaɗa rahoton ƙarya a kaina ba don kawai suyi suna."

A wani labarin kuma Jagoran APC Bola Tinubu Yayi Zazzafan Martani Ga Masu Son Ɓallewa Daga Najeriya

Jigon jam'iyya mai Mulki APC, Bola Tinubu, yayi kira ga masu son a raba ƙasar nan da su kwantar da hankalinsu, Najeriya tafi kyau idan ta kasance a haɗe.

Tinubu ya gargadesu da kada su biye wa dokin zuciyarsu wajen shiga yaƙin da ba'a san ƙarshensa ba, yace kada suyi ƙoƙarin maida Najeriya kamar Sudan ko Iraqi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel