Jagoran APC Bola Tinubu Yayi Zazzafan Martani Ga Masu Son Ɓallewa Daga Najeriya

Jagoran APC Bola Tinubu Yayi Zazzafan Martani Ga Masu Son Ɓallewa Daga Najeriya

- Jigon jam'iyya mai Mulki APC, Bola Tinubu, yayi kira ga masu son a raba ƙasar nan da su kwantar da hankalinsu, Najeriya tafi kyau idan ta kasance a haɗe

- Tinubu ya gargadesu da kada su biye wa dokin zuciyarsu wajen shiga yaƙin da ba'a san ƙarshensa ba, yace kada suyi ƙoƙarin maida Najeriya kamar Sudan ko Iraqi

- Hakanan kuma, tsohon gwamnan Lagas ɗin ya yabawa gwamnan jihar, Babajide Sanwo-Olu, da mataimakinsa bisa kawo cigaba a faɗin jihar

Jigon jam'iyyar APC na ƙasa, Asiwaju Bola Tinubu, yayi kira ga waɗanda keson a raba ƙasar nan dasu jefar da wannan kudirin nasu, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: An Cinna wa Ofishin INEC Wuta a Jihar Akwa Ibom, Kayayyakin Zaɓen Sun Ƙone

A jawabin fatan alkairi da yayi a wurin lakcar watan ramadana ta musamman wacce ta gudana a Marina, jihar Lagos, Tinubu ya jaddada cewa Najeriya tafi kyau iɗan tana haɗe.

Yace wasu mutane na ƙoƙarin buga gangar yaƙi, to su sani ba abinda yaƙi zai jawo mana face rikice-rikice kamar yadda ƙasashen Sudan da Iraqi suke ciki.

Jagoran APC Bola Tinubu Yayi Zazzafan Martani Ga Masu Son Ɓallewa Daga Najeriya
Jagoran APC Bola Tinubu Yayi Zazzafan Martani Ga Masu Son Ɓallewa Daga Najeriya Hoto: @AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

A cewar Bola Tinubu har yanzun Najeriya bata gama farfaɗowa daga yaƙin da tayi ba a baya, Sabida haka, bai kamata a bari ta sake fuskantar wani yaƙin ba.

A jawabin nasa Jagoran APC ɗin yace:

"Allah ba zai bari Najeriya ta sake faɗawa cikin yaƙi ba, idan mukace muna son a raba Najeriya ta dole, to yakamata mutanenmu su rinƙa tunawa da abinda yaƙi ya jawo ma kasar Sudan da kuma Iraq."

KARANTA ANAN: Ku Kawar da Mulkin APC Idan Baku Gamsu Ba Da Shi Ba, Gwamnan APC Ya Baiwa Matasa Shawara

"Najeriya tafi kyau idan tana a haɗe, bani da wata ƙasa sai Najeriya, duk wanda yasan abunda ya faru a waccan yaƙin, bazai so ayi yaƙi ba yanzun. Muna addu'a Allah yakawo zaman lafiya a ƙasar nan da kyakkyawar kulawar lafiya, bawai araba Najeriya ba."

Tinubu ya kuma yabawa gwamnan jihar Lagos, Mr. Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa, Dr. Obafemi Kadiri, bisa nasarorin da suka samu a lokacin mulkinsu.

Yace jahar Lagos ta samu cigaba mai ɗinbin yawa a ƙarƙashin mulkin gwamnatin, Sanwo-Olu.

A wani labarin kuma Sanatoci Sun Bayyana Dalilinsu Na Tantance Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Pantami

Majalisar dattijai ta bayyana cewa babu wani mutum ko wata ƙungiya da ta kawo mata ƙwaƙƙwarar hujja wanda zata bada damar a sallami ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Dr. Ajibola Basiru, shine ya bayyana haka a wata hira da yayi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262