Yahaya Bello: Buhari na kaunar matasan Najeriya, yana basu dama masu yawa

Yahaya Bello: Buhari na kaunar matasan Najeriya, yana basu dama masu yawa

- Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi yace shugaban kasa Buhari yana matukar kaunar matasan Najeriya

- Bello yace soyayyar ta fara bayyana ne tun bayan da yasa hannu a kan kudirin rage shekarun masu neman kujerar siyasa

- Bello ya bukaci matasa da su hada kai tare da ganin cewa sun karba ragamar kasar nan tunda dattawa da yayyinsu sun gaza

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari tana kaunar matasa kuma tana son ganinsu a cikin harkar shugabanci.

Gwamnan yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na kauna kuma yana fifita matasa a kasar nan inda ya kara da cewa hakan alama ce dake nuna goyon bayansa ga bukatar baiwa matasa mulki.

A watan Mayun 2018 shugaban kasan yasa hannu a kan kudirin rage shekarun takarar majalisar jiha da majalisar wakilai daga 30 zuwa 25, majalisar dattawa da gwamnoni daga 35 zuwa 30 da kuma kujerar shugaban kasa daga 40 zuwa 35.

KU KARANTA: Batanci ga Annabi: Fusatattun matasa sun lallasa kwamandan 'yan sintiri, sun kone motarsa

Yahaya Bello: Buhari na kaunar matasan Najeriya, yana basu dama masu yawa
Yahaya Bello: Buhari na kaunar matasan Najeriya, yana basu dama masu yawa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ganduje ya karawa malaman makaranta shekarun ritaya, daga 60 zuwa 65

A yayin zantawa da shirin gari ya waye na gidan talabijin na Channels a ranar Talata, Bello yace lokaci yayi da matasa zasu karba ragamar mulkin kasar nan.

"Mun san cewa shugaban kasa yana matukar kaunar matasan Najeriya, shugabannin ne suka batar damu a baya. Shugaban kasa ya yanke shawarar cewa zai yi iyakar kokarinsa wurin ganin matashi ya karba ragamar mulkin kasar nan," yace.

”Kun ga shugaban EFCC a yanzu. Yanzu ne lokacin da ya dace mu bar matasa su karba kasar nan kuma su gyarata. Idan shugabanninmu, dattawa da yayyinmu sun kasa, ai bamu yi yarinta da zamu gaza ba.

"Kada hankulanmu su karkata ga matsalar tsaro da wasu kanana lamurra. Mu hada kanmu tare da karfinmu wurin ganin mun gyara kasar nan."

A wani labari na daban, farar hula shida tare da jami'in tsaro daya ne suka rasa rayukansu yayin da mayakan Boko Haram suka kai farmaki garin Ajari dake karamar hukumar Mafa ta jihar Borno a ranar Litinin.

Karamar hukumar Mafa ce inda Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya fito. Kamar yadda sakataren karamar hukumar, Mohammed Sherrif, yace, "'Yan ta'addan sun tsinkayi garin wurin karfe 1 na dare kuma suka dinga bankawa gidajen jama'a wuta sannan suka kashe farar hula shida da wani jami'in tsaro daya."

Mafa tana da nisan kusan kilomita 30 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno, jaridar The Punch ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel