Ganduje ya karawa malaman makaranta shekarun ritaya, daga 60 zuwa 65

Ganduje ya karawa malaman makaranta shekarun ritaya, daga 60 zuwa 65

- Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano, ya karawa malaman makaranta shekarun yin ritaya

- Ya kara daga shekaru 60 zuwa 65 kuma hakan zai shafi dukkan malaman dake aiki a karkashin jihar ne

- Gwamnan yace malamai zasu iya aiki har tsawon shekaru 40 ba 35 ba kuma zai tabbatar da ingancin walwalarsu

Gwamnan jihar kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya kara shekarun ritaya na malaman makarantu har da na gaba da sakandare a jihar daga 60 zuwa 65.

Ganduje ya sanar da hakan ne a wata liyafar dare ta karramawa da aka yi domin bikin shagalin ranar Mayu wacce kungiyar kwadago ta jihar Kano ta shirya a ranar Asabar.

Kamar yadda The Cable ta ruwaito, gwamnan ya kara shekarun aikin malaman makarantan daga 35 zuwa 40.

"Tuni gwamnatin tarayya ta amince da hakan ga malamai da kuma malaman makarantun gaba da sakanadare, hakan ne yasa ba a bar gwamnatin Kano ba a baya," cewar ganduje.

KU KARANTA: Shigar Boko Haram Abuja: 'Yan sandan FCT sun magantu, an fara sintiri babu kakkautawa

Ganduje ya karawa malaman makaranta shekarun ritaya, daga 60 zuwa 65
Ganduje ya karawa malaman makaranta shekarun ritaya, daga 60 zuwa 65. Hoto daga @TheCableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Kayatattun Hotunan katafaren filin jiragen sama na China ya bar mutane baki bude

"A don haka, daga yanzu malamai zasu fara morar sabuwar shekarar ritaya daga 60 zuwa 65 kuma zasu iya aiki na shekaru 35 zuwa 40 kamar yadda malaman tarayya ke morewa."

Ya kara da cewa gwamnatin jihar ta gabatar da sabbin sauye-sauye domin inganta walwalar ma'aikatanta.

"Mun gabatar da cibiyar tarin kudi na kula da lafiyar ma'aikatanmu da iyalinsu kuma zasu mori ayyukan lafiya a cikin arha." yace.

"Ina farin ciki da hadin kanku, a yau muna da cibiyar kula da lafiyar ma'aikata mafi inganci a Najeriya.

"Muna kara hada kai da ma'aikatu masu zaman kansu a jihar domin ganin yadda zaku mora daga su a karkashin wannan hukumar tare da karfafa sabin dokokinta."

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin kudin 'yan fansho zuwa sabon karancin albashin kasar nan da aka duba a watan Afrilun 2019.

Ekpo Nta, mukaddashin shugaban hukumar albashi ta kasa (NSIWC) ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a garin Kalba, babban birnin jihar Cross Rivers a ranar Juma'a.

A watan Afirlun 2019, Buhari ya sa hannun kan sabuwar dokar karancin albashi. An kara daga N18,500 zuwa N30,000 a matsayin mafi karancin albashi a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: