Batanci ga Annabi: Fusatattun matasa sun lallasa kwamandan 'yan sintiri, sun kone motarsa

Batanci ga Annabi: Fusatattun matasa sun lallasa kwamandan 'yan sintiri, sun kone motarsa

- Fusatattun matasa sun kone mota, ofishi tare da farfasa gidan wani kwamandan 'yan sintiri a Legas

- Ana zargin Haladu Mohammed, mazaunin Gangare da yin kalaman batanci ga annabi Muhammad

- Ko bayan zuwan jami'an tsaron, matasan yankin sun hada dasu inda suka raunata sauran yaran kwamandan, shi kuwa ya sha da kyar

An samu hargitsi da tashin hankali a yankin Gangare na fitacciyar kasuwar Mile 12 dake karamar hukumar Kosefe na jihar Legas a ranar Juma'a bayan an zargi wani kwamandan 'yan sintiri mai suna Haladu Muhammed da yi wa Annabi batanci.

Daily Trust ta tattaro yadda wasu fusatattun matasa suka zargesa da yin kalaman batanci ga Annabi Muhammad, lamarin da yasa suka kai masa farmaki.

Kafin jami'an tsaro su kaiwa wanda ake zargin dauki, an kone motarsa kuma an farfashe gidansa.

Wani ganau ba jiyau ba mai suna Usman Adam Sarauta, ya tabbatar da cewa matasan sun hada da jami'an tsaron da suka gaggauta zuwa wurin bayan kiransu da aka yi.

KU KARANTA: Mbaka ya bukaci kwangila bayan goyon bayan Buhari amma aka hana shi, Garba Shehu

Batanci ga Annabi: Fusatattun matasa sun lallasa kwamandan 'yan sintiri a Legas
Batanci ga Annabi: Fusatattun matasa sun lallasa kwamandan 'yan sintiri a Legas. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kayatattun Hotunan katafaren filin jiragen sama na China ya bar mutane baki bude

"Sun zargesa da yin amfani da kalamai marasa dadi a kan ma'aikin Allah, amma ba mu tabbatar ba. Allah ne kadai ya san gaskiyar lamarin.

"Na ga yadda suka farfsashe gidansa da ofishinsa kuma suka kone motarsa. Ina zama a yankin kuma na gano yadda mazauna yankin ke korafi da halayyar kwamandan 'yan sintirin. Wasu na zarginsa da yi musu rashin mutunci, zai yuwu hade masa kai suka yi," yace.

Wani shaida mai suna Muhammad ya ce shi kanshi kwamandan da kyar ya sha daga hannun matasan amma wasu daga cikin yaransa duk sun samu raunika.

"Aan gano cewa da kyar kwamandan ya sha bayan wasu jami'an tsaro sun kai masa dauki, amma wasu daga cikin 'yan sintirin sun ji jiki. Wasu na cewa an yi kisa amma babu shaidar hakan.

“An ga matasan da yawansu suna jefa duwatsu kuma an ga harsashi ya samu wata mata wacce a take ta mutu."

A wani labari na daban, rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, ta musanta rade-radin da ake yi na cewa mayakan Boko Haram sun kai farmaki babban birnin kasar Najeriya.

Ana ta yadawa cewa Boko Haram sun kai hari Abuja bayan samun su da aka yi a jihar Neja dake makwabtaka da su, The Cable ta ruwaito.

Yusuf Mariam, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, ta ce an ga jama'a masu yawa a babura a wasu sassan babban birnin tarayyan, lamarin da ya kawo wannan rade-radin kuma yasa jami'ansu suna fita sintiri.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel