Rashin Tsaro: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 a Wani Sabon Hari a Jihar Benuwai

Rashin Tsaro: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 a Wani Sabon Hari a Jihar Benuwai

- Akalla mutane 17 ne suka rasa rayuwarsu a wasu jerin hare-hare da yan bindiga suka kai wasu ƙauyuka a jihar Benuwai

- Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan ɗauke da muggan makamai sun kai harin ne ranar Lahadi da yamma da kuma Litinin da safe

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar Lamarin amma tace bata da cikakken bayani a kan abinda ya faru yayin da yan bindigan suka kai harin

Aƙalla mutane 17 ne suka rasa rayukansu bayan wasu mutane ɗauke da makamai sun mamaye wasu ƙauyuka a ƙaramar hukumar Gwer ta yamma a jihar Benuwai, kamar yadda Dailytrust ruwaito.

KARANTA ANAN: Salon Mulkin Buhari Ne Zai Tarwatsa Najeriya, Tsohuwar Minista Ta Caccaki DSS

Rahotanni sun tabbatar da cewa an kai hare-haren ne da yammacin ranar Lahadi da kuma safiyar ranar Litinin.

Maharan sun kai hari ne a ƙauyuka da dama na ƙaramar hukumar Gwer ta yamma, daga ciki harda ƙauyen Agbanu, dake kan hanyar Naka-Agagbe, inda mutum biyu suka rasa ransu.

Rashin Tsaro: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 a Wani Sabon Hari a Jihar Benuwai
Rashin Tsaro: Wasu Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 17 a Wani Sabon Hari a Jihar Benuwai Hoto: thenigeriadaily.com
Asali: UGC

Wani shaida ya tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun kai farmaki ƙauyen Tse Amgbem dake kusa da garin Aondoana ƙaramar hukumar Gwer, inda suka kashe mutane 15.

KARANTA ANAN: Yan Najeriya Zasu Sami Kwanciyar Hankali a Mulkin Buhari, Bola Tinubu

Shaidan ya kuma ce mutane da dama sun samu raunuka a harin yayin da maharan suka cinnawa gidaje da yawa wuta.

Wani mazaunin garin yace: "Akwai yuwuwar a sake gano wasu gawarwaki da dama nan gaba, saboda har yanzun akwai mutane da yawa da suka ɓata bayan harin."

Da aka tuntuɓi mai magana da yawun yan sandan jihar ta Kogi, DSP Catherine Anene, ta tabbatar da cewa sun sami rahoton kai hare-haren amma bata da cikakken bayani a kan abinda ya faru yayin harin.

A wani labarin kuma Jagoran APC Bola Tinubu Yayi Zazzafan Martani Ga Masu Son Ɓallewa Daga Najeriya

Jigon jam'iyya mai Mulki APC, Bola Tinubu, yayi kira ga masu son a raba ƙasar nan da su kwantar da hankalinsu, Najeriya tafi kyau idan ta kasance a haɗe.

Tinubu ya gargadesu da kada su biye wa dokin zuciyarsu wajen shiga yaƙin da ba'a san ƙarshensa ba, yace kada suyi ƙoƙarin maida Najeriya kamar Sudan ko Iraqi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel