Muna tare da shugaba Buhari, Hedkwatar Soji ta yi watsi da shawaran juyin mulki

Muna tare da shugaba Buhari, Hedkwatar Soji ta yi watsi da shawaran juyin mulki

- Hukumar Sojojin Najeriya ta bayyana biyayyarta ga shugaba Muhammadu Buhari da kundin tsarin mulkin Najeriya

- Hedkwatar tsaro ta shawarci yan siyasa da jami'an tsaro su yi biyayya ga Demokradiyya

- Gwamnatin Buhari na shan caccaka biya tabarbarewar tsaro a fadin tarayya

Hedkwatar tsaro (DHQ) ta gargadi Sojoji da yan siyasa kan suyi hattara da kowani irin shirin yiwa gwamnatin shugaba Buhari juyin mulki.

Kakakin hedkwatar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya yi wannan gargadi ne a jawabin da ya saki a Abuja ranar Lahadi, 3 ga Mayu, PRNigeria ta ruwaito.

Nwachukwu ya ce hukumar Soji ta samu labarin cewa wani ya bada shawaran mika mulki ga Sojoji domin yiwa kasa garambawul.

A cewarsa, wani lauya, Robert Clark (SAN) ne yayi jawabin.

DHQ ta yi watsi da wannan kira da yake yi na mika mulki ga Soji kuma ta jaddada cewa tana mubaya'a ga mulkin demokradiyya.

DUBA NAN: An Kama Soja da Harsashi Sama da 2000 a Tashar Mota a Maiduguri

Muna tare da shugaba Buhari, Hedkwatar Soji ta yi watsi da shawaran juyin mulki
Muna tare da shugaba Buhari, Hedkwatar Soji ta yi watsi da shawaran juyin mulki Credit: Femi Adesina
Asali: Facebook

KU KARANTA: Wasu Malaman addini da tsaffin yan siyasa na son yiwa Buhari juyin mulki, Fadar shugaban kasa

Wani sashen jawabin yace: "Bari mu bayyana a fili cewa Sojojin Najeriya na biyayya ga gwamnatin nan da dukkan hukumomin demokradiyya."

"Zamu cigaba da nisanta kanmu daga siyasa, da kuma biyayya ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kundin tsarin mulkin 1999."

Hukumar ta karashe jawabinta da cewa hukumomin tsaro na iyakan kokarinsu wajen dakile matsalolin rashin tsaron da suka addabi kasar.

A bangare guda, babban malamin addini, Sheikh Ahmad Gumi, ya bayyana cewa yan ta'addan Boko Haram ne suka sace daliban Greenfield dake Kaduna ba yan bindiga ba.

An yi garkuwa da daliban ne a ranar 20 ga watan Afrilu 2021, a makarantarsu dake Kaduna.

Tun lokacin aka yanke cewa yan bindiga masu garkuwa da mutane ne suka sace yaran.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng