Minista Ya Bayyana Matakin da Yakamata a Ɗauka Kan Gwamnonin da Suka Ƙi Biyan Mafi Ƙarancin Albashi

Minista Ya Bayyana Matakin da Yakamata a Ɗauka Kan Gwamnonin da Suka Ƙi Biyan Mafi Ƙarancin Albashi

- Ministan ƙwadugon ƙasar nan, Dr. Chriss Ngige, yace duk wani gwamna da ya kasa biyan mafi ƙarancin albashi to ya sani ya karya dokar ƙasa

- Ministan yayi wannan jawabi ne yayin da yake zantawa a cikin wani shirin kafar yaɗa labarai, yace dokar tace wajibine a biya ma'aikaci mafi ƙarancin Albashi

- Dokar ta bada izinin gurfanar da duk wani wanda ya kasa biyan ma'aikatansa mafi ƙarancin albashi na N30,000 a gaban kotu domin a baiwa ma'aikacin haƙƙinsa

Ministan ƙwadugo na ƙasa, Chris Ngige, yayi Allah wadai da wasu gwamnoni bisa ƙin biyan mafi ƙarancin albashi a jihohinsu.

KARANTA ANAN: Sanatoci Sun Bayyana Dalilinsu Na Tantance Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Pantami

A yayin da yake jawabi a cikin shirin channels TV na 'Sunday Politics' Ministan yace duk wani mai ɗaukar aiki, wanda yake biyan ma'aikatansa ƙasa da N30,000, to ya karya dokar ƙasar nan.

Minista Ya Bayyana Matakin da Yakamata a Ɗauka Kan Gwamnonin da Suka Ƙi Biyan Mafi Ƙarancin Albashi
Minista Ya Bayyana Matakin da Yakamata a Ɗauka Kan Gwamnonin da Suka Ƙi Biyan Mafi Ƙarancin Albashi Hoto: @SenChrisNgige
Asali: Twitter

Ministan yace:

"Idan ka karanta dokar da kyau to tabbas zakaga abinda ta ƙunsa, ɗaya daga cikin amfanin dokar shine, a ɓangaren ƙasa (Sashi na 2), inda dokar tace wajibi ne a biya ma'aikaci N30,000."

"Idan kadiba anyi amfani da kalmar wajibi, saboda haka dokar bata bada dama ko kaɗan na yin zaɓi ba, dolene biyan mafi ƙarancin albashin. Duk wasu gwamnoni da basu biyan wannan mafi ƙarancin albashin to sun karya doka."

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Boko Haram Sun Sake Kai Hari Wata Ƙaramar Hukuma a Jihar Borno

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sawa dokar mafi ƙarancin albashin hannu a ranar 18 ga watan Afrilu, kuma daga lokacin ta zama cikakkiyar doka.

Dokar tace: "Wajibine ga duk wani da ya ɗauki ma'aikata suke masa aiki, ya biyasu mafi ƙarancin albashi N30,000. Idan aka biya ƙasa da haka to ma'aikatan na da damar kai ƙara Kotu don abi musu haƙƙinsu."

"Hakanan Mahukunta kamar ministan ƙwadugo da sauran ministoci, suna da damar ɗaukar hukunci akan lamarin amadadin ma'aikacin, domin a dawo masa da haƙƙinsa."

A wani labarin kuma Gwamnonin Arewa Sun Bayyana Matsayarsu a Kan Zargin Da Akewa Sheikh Pantami

Ƙungiyar gwamnonin arewa tayi martani a kan kace-nace da ake tayi kan wasu kalamai da ministan Sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami, yayi a baya.

Gwamnonin sun bayyana cewa basu son a saka su a cikin lamarin, domin a cewarsu basu da alaƙa da irin waɗannan kalaman.

Asali: Legit.ng

Online view pixel