Da Ɗuminsa: Boko Haram Sun Sake Kai Hari Wata Ƙaramar Hukuma a Jihar Borno

Da Ɗuminsa: Boko Haram Sun Sake Kai Hari Wata Ƙaramar Hukuma a Jihar Borno

- Wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun kai hari ƙauyen Ajiri dake ƙaramar hukumar Mafa a jihar Borno da sanyin safiyar nan ta yau Lahadi

- Rahotanni sun bayyana cewa yan ta'addan sun sami nasarar shiga sansanin sojojin Najeriya dake yankin kuma suka kore su daga wurin

- Wani jami'in tsaro ya tabbatar da kai harin amma yace bazai yuwu su bada cikakken bayani akan harin ba a halin yanzu saboda wasu dalilai na tsaro

Wasu da ake zargin mayaƙan ƙungiyar Boko Haram ne sun mamaye ƙauyen Ajiri ƙaramar hukumar Mafa a jihar Borno da sanyin safiyar Lahadi, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Wasu mazauna Geidam sun bayyana yadda yan Boko Haram ke musu wa'azi bayan sun ƙwace iko

A harin dai mayaƙan sun sami nasarar shiga sansanin sojojin dake wajen kuma suka kore su daga sansanin.

Wannan harin na zuwa ne bayan awanni 12 kacal da tawagar wasu yan ta'adda suka kai hari ƙauyen garin Rann, inda hedkwatar ƙananan hukumomin Balge da Goza suke a jihar.

Da Ɗuminsa: Boko Haram Sun Sake Kai Hari Wata Ƙaramar Hukuma a Jihar Borno
Da Ɗuminsa: Boko Haram Sun Sake Kai Hari Wata Ƙaramar Hukuma a Jihar Borno Hoto: time.com
Asali: UGC

Kauyen Ajiri nada nisan kilomita 50 daga tsakiyar Borno, kauyen na kan hanyar Maiduguri-Mafa-Dikwa wanda mafiyawancin mutanen wajen sun barshi saboda rashin tsaro, amma sun koma kwanan nan domin su ɗauki kayyyakin amfaninsu.

Wani babban ma'aikacin hukumar tsaro ya tabbatar da harin da yan ta'addan suka kai yankin Ajiri, Rann da kuma Limkara.

Sai-dai ya bayyana cewa bazai yuwu ya bayar da cikakken bayani akan hare-haren ba saboda lalurar tsaro.

KARANTA ANAN: Sakataren Amurka yayi magana kan matsalar tsaro bayan ganawarsa da Shugaba Buhari

A kwanan nan dai, mayakan Ƙungiyar Boko Haram sun tasarma jihar Borno da maƙociyarta Yobe da yawan kai hare-hare, inda kwanakin bay suka kai wani mummunan hari garin Geidam dake jihar Yobe.

Rahotanni sun bayyana cewa a harin da suka kai Geidam har saida suka kafa tutocin su a wasu yankunan garin, kuma suka bi gida-gida suka kira ga matasa su shigo ƙungiyarsu.

A wani alabarin kuma Gwamnatin Kaduna ta bayyana dalilin da yasa yan bindiga suka dirar ma Jihar da ta'addanci

Gwamnatin jihar Kaduna ta yi Allah wadai da kisan da yan bindiga keyiwa ɗalibai masu karatu a makarantun gaba da sakandire na Jihar.

Gwamnatin tace yan bindigar na haka ne don kawai su jawo hankalinta ta canza matsayarta na 'Ba biyan kuɗin fansa' da kuma 'Ba maganar sulhu da yan bindiga'.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel