Sanatoci Sun Bayyana Dalilinsu Na Tantance Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Pantami

Sanatoci Sun Bayyana Dalilinsu Na Tantance Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Pantami

- Majalisar dattijai ta bayyana dalilin da yasa Ministan sadarwa ya tsallake tantancewarsu

- Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Dr. Ajibola Basiru, shine ya bayyana haka a wata hira da yayi a Abuja

- Yace kodama ace akwai wannan rahoton lokacin da majlisar ke aikin tantance ministocin, babu wata doka da zatasa a hana ɗora shi a muƙamin bisa rahoton kafar sada zumunta

Majalisar dattijai ta bayyana cewa babu wani mutum ko wata ƙungiya da ta kawo mata ƙwaƙƙwarar hujja wanda zata bada damar a sallami ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami.

KARANTA ANAN: Dalilin da Yasa Zamu Cire Tallafin Man Fetur, Gwamnatin Tarayya Tayi Bayani

Tun bayan bayyanar wasu kalamai da ministan yayi a baya da suke nuna yana goyon bayan wasu ƙungiyoyin yan ta'addan duniya, Pantami ya cigaba da shan suka da kuma kiran ya sauka daga muƙaminsa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Wasu yan Najeriya da ƙungiyoyin addinai sun buƙaci ministan ya fita daga cikin majalisar zartarwar shugaba Muhammadu Buhari, yayin da wasu ke ganin ya cigaba da riƙe muƙaminsa.

Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sanatoci Sun Bayyana Goyon Bayan Su Ga Ministan Sadarwa Sheikh Isa Pantami
Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sanatoci Sun Bayyana Goyon Bayan Su Ga Ministan Sadarwa Sheikh Isa Pantami Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Amma a yayin da yake zantawa da jaridar 'Punch Sunday' a Abuja, shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dattijai, Dr. Ajibola Basiru, yace bai kamata a zargi majalisar su ba dan ta tantance ministan lokacin da aka naɗa shi.

Yace duk da kasancewar ba'a kawowa majalisar wani ƙorafi a kan minitan ba, babu wani rahoton tsaro da ya zargi ministan da wani abu a lokacin da aka tatantance shi.

Basiru ya ƙara da cewa babu wani ƙorafi da aka turawa majalisar dake zargin ministan tun bayan da lamarin ya fara yawo a wajen jama'a makonnin da suka gabata.

Yace duk da wannan raɗe-raɗin da ake ta yawo dashi a kan ministan, babu wata doka da ta bayarda damar sallamar shi, Shugaba Buhari ne kaɗai keda karfin ikon yin hakan.

Basiru yace:

"Bari in fara tabbatar muku da cewa, babu wani abu da ya hana shi (Pantami) neman takarar zaɓe a kundin tsarin mulkin Najeriya. Majalisar dattijai tayi aiki ne bisa bayanan da ta samu a lokacin tantance ministan, ba zamu yi abunda ya saɓa ma doka ba."

KARANTA ANAN: Rashin Tsaro: APC Ta Maida Zazzafan Martani Ga Gwamnonin PDP

"Babu wata hukumar tsaro a ƙasar nan data kawo mana wani rahoto ko wani bayani a kansa lokacin tantance shi, wanda zai hana shi riƙe wannan muƙamin, tun a wancan lokacin har zuwa yanzun."

"Majalisar dattijai bata da ikon tunɓuke minista, aikinmu kawai shine mu tantance duk wanda aka turo mana bisa bayanan da muka samu daga hukumomin tsaro, babu yadda za'ai muyi aiki da rahoton da aka samu daga kafar sada zumunta."

Basiru ya kuma ƙara da cewa: "Shugaba Buhari ne kaɗai keda ikon saukewa ko kuma naɗa minista. Duk waɗannan da suke ta magana akai, basu da wata doka da zasu nuna wacce za'a yi amfani da ita a sauke ministan."

"Koda ma ace akwai waɗannan bayanan tun lokacin da za'a tantance minista Pantami, shin akwai wata doka da zata hana tantanceshi saboda rahoton kafar sada zumunta a ƙarƙashin dokokin Najeriya?"

Ya kuma yi watsi da kiraye-kirayen da wasu keyi a sauke ministan daga muƙaminsa, yace jita-jita abu ne sananne a siyasance.

A wani labarin kuma Cikakken Bayani: Dalilin Da Yasa JAMB Ta Buɗe Cibiyoyin Dake Maguɗin Jarabawa

Shugaban Hukumar JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana dalilin da yasa hukumar su ta buɗe cibiyoyin maguɗin jarabawa.

Yace sun yi haka ne domin ɗana tarko ga ɗaliban da suke da shirin yin maguɗi, da zarar sun kama mutum zasu koreshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel