Da Ɗumi-Ɗumi: An Cinna wa Ofishin INEC Wuta a Jihar Akwa Ibom, Kayayyakin Zaɓen Sun Ƙone

Da Ɗumi-Ɗumi: An Cinna wa Ofishin INEC Wuta a Jihar Akwa Ibom, Kayayyakin Zaɓen Sun Ƙone

- An cinna wa Wani ofishin hukumar zaɓe ta ƙasa wuta a jihar Akwa Ibom, Kwamishinan hukumar INEC na jihar ya tabbatar da faruwar lamarin

- Wannan na ƙunshe ne a wani sako da INEC ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita.

- Hukumar tace irin waɗannan hare-haren ka iya maidawa INEC hannun agogo baya yayin da take gudanar da shirye-shiren babban zaɓe mai zuwa a shekarar 2023

Wani Ofishin ƙaramar hukuma na hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) a jihar Akwa Ibom ya kama da wuta. Kwamishinan zaɓen jihar, Barr. Mike Igini, ya tabbatar da faruwar lamarin.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Boko Haram Sun Sake Kai Hari Wata Ƙaramar Hukuma a Jihar Borno

Legit.ng ta ruwaito cewa, INEC ta bayyana haka a wani sako da ta fitar a shafinta na dandalin sada zumunta Tuwita.

Hukumar zaɓen tace Wutar ta kama ne da sanyin safiyar yau Lahadi, 2 ga watan Mayu, 2021 a ofishinta dake ƙaramar hukumar Essien Udim, jihar ta Akwa Ibom.

Da Ɗumi-Ɗumi: An Cinna wa Ofishin INEC Wuta a Jihar Akwa Ibom, Kayayyakin Zaɓen Sun Ƙone
Da Ɗumi-Ɗumi: An Cinna wa Ofishin INEC Wuta a Jihar Akwa Ibom, Kayayyakin Zaɓen Sun Ƙone Hoto: @Inecnigeria
Asali: Twitter

Jawabin da hukumar tayi ya nuna cewa wutar tayi ɓanna a ofishin inda ta lalata Akwatunan zaɓe guda 345, da kuma teburan jefa kuri'a 135, wayoyin hannu, tankin ruwa da kuma kayayyakin cikin ofis ɗin.

Rundunar yan sanda, waɗanda suma suke fama da irin wannan harin, sun san da faruwar lamarin kuma sun fara bincike a kan lamarin.

KARANTA ANAN: Jami'an Kwastam Sun Kai Samame Wata Kasuwa a Ibadan, Sun Ƙwace Buhunan Shinkafa

INEC tace: "Waɗannan hare-haren da ake kaiwa kwanan nan akan kayayyakinmu bayan mun kammala kai kayayyakin zaɓe a faɗin ƙasar nan saboda ƙaratowar zaɓen 2023 abun damuwa ne matuƙa."

"Idan ba'a cigaba da kulawa yadda yakamata ba, Waɗannan hare-haren zasu iya maida mana hannun agogo baya a kan dukkan ayyuakan da hukumar tasa a gaba, waɗanda suka haɗa da; cigaba da gunanar da rijistar cancantar jefa ƙuri'a da sauran su."

"Amma duk da haka, hukumar na tabbatarwa yan Najeriya cewa zata maida komai yadda yake kafin faruwar lamarin a Akwa Ibo., kuma zata cigaba da shirye-shiryen zaɓe yadda yakamata."

A wani labarin kuma Sanatoci Sun Bayyana Dalilinsu Na Tantance Ministan Sadarwa, Sheikh Isa Pantami

Majalisar dattijai ta bayyana cewa babu wani mutum ko wata ƙungiya da ta kawo mata ƙwaƙƙwarar hujja wanda zata bada damar a sallami ministan sadarwa da tattalin arziƙin zamani, Isa Pantami.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar, Dr. Ajibola Basiru, shine ya bayyana haka a wata hira da yayi a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel