Shigar Boko Haram Abuja: 'Yan sandan FCT sun magantu, an fara sintiri babu kakkautawa

Shigar Boko Haram Abuja: 'Yan sandan FCT sun magantu, an fara sintiri babu kakkautawa

- Rundunar 'yan sanda babban birnin tarayya ta musanta rade-radin shigar Boko Haram garin

- Kamar yadda kakakin rundunar, Mariam Yusuf ta sanar, a halin yanzu jami'an tsaro sun tsananta sintiri

- Ta tabbatar da cewa taron da aka yi na hukumomin tsaro na ranar Alhamis da ta gabata zai kawo karshen ta'addanci a FCT

Rundunar 'yan sandan babban birnin tarayya, ta musanta rade-radin da ake yi na cewa mayakan Boko Haram sun kai farmaki babban birnin kasar Najeriya.

Ana ta yadawa cewa Boko Haram sun kai hari Abuja bayan samun su da aka yi a jihar Neja dake makwabtaka da su, The Cable ta ruwaito.

Yusuf Mariam, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan, ta ce an ga jama'a masu yawa a babura a wasu sassan babban birnin tarayyan, lamarin da ya kawo wannan rade-radin kuma yasa jami'ansu suna fita sintiri.

KU KARANTA: Da duminsa: IGP ya sauyawa manyan 'yan sandan kudu maso gabas wurin aiki

Shigar Boko Haram Abuja: 'Yan sandan FCT sun magantu, an fara sintiri babu kakkautawa
Shigar Boko Haram Abuja: 'Yan sandan FCT sun magantu, an fara sintiri babu kakkautawa. Hoto daga @Thenation
Asali: UGC

KU KARANTA: Ndume: Najeriya bata mayar da hankali ba wurin shawo kan matsalar tsaro

A wata takarda da ta fitar a ranar Lahadi, Mariam tace an fara tsananta sintiri kuma hakan yana daga cikin matsayar da aka cimmawa bayan taron hadin guiwa na jami'an tsaro da aka yi a ranar Alhamis.

Ta ce: "Hankalin jami'an tsaron hadin guiwa na FCT kan wata wallafa dake yawo wacce tace miyagun 'yan ta'addan Boko Haram sun kai hari babban birnin tarayya.

"Jami'an tsaron hadin guiwan na sanar da cewa babu gaskiya a cikin wannan wallafar kuma an yi ta ne domin gigita jama'a mazauna babban birnin tarayyan.

“Akasin wannan hasashen, shugabannin cibiyoyin tsaro na babban birnin tarayyan sun tashi domin shawo kan matsalar tsaron da ta addabi garin kuma hakan yasa suka yi taro a ranar Alhamis, 29 ga watan Afirilun 2021.

"Kungiyar ta yanke hukuncin tura jami'an sintiri yankunan da matsalar tsaron ta fi addaba.

“Hukumomin tsaron sun fara aiki da babura, dawaki da sauran hanyoyin samo bayanai domin bankado dukkan matsalar tsaro ta babban birnin."

Bala Ciroma, kwamishinan 'yan sandan jihar, yayi kira ga mazauna garin da su kwantar da hankulansu sannan su kasance masu kiyaye doka.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin kudin 'yan fansho zuwa sabon karancin albashin kasar nan da aka duba a watan Afrilun 2019.

Ekpo Nta, mukaddashin shugaban hukumar albashi ta kasa (NSIWC) ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a garin Kalba, babban birnin jihar Cross Rivers a ranar Juma'a.

A watan Afirlun 2019, Buhari ya sa hannun kan sabuwar dokar karancin albashi. An kara daga N18,500 zuwa N30,000 a matsayin mafi karancin albashi a kasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: